Matakai 2 da Shugaba Tinubu Ya Dauka Sun Sa Za a Adana Naira Tiriliyan 8 a Shekara
- Taiwo Oyedele ya ce a dalilin daina biyan tallafin man fetur ga ‘yan kasuwa, an huta da kashe N4tr
- Shugaban kwamitin gyaran harajin ya ce daidaita farashin kudin kasashen waje ya taimaki kasar
- Tsare-tsaren da aka kawo sun ba gwamnatin tarayya damar adana N8tr a kowace shekara a yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Lagos - Shugaban kwamiti na musamman da aka kafa domin gyara harkar haraji a Najeriya, Taiwo Oyedele, ya yi wa al’umma albishir.
Punch ta ce Taiwo Oyedele ya ce a sakamakon cire tallafin fetur da na kudin kasar waje, gwamnati za ta rika adana N8tr a duk shekara.
Taiwo Oyedele ya yi wannan bayani ne a wajen wani taro da kungiyar LCCI ta shirya domin tattaunawa a kan kundin kasafin kudin 2024.
Betta: Gbajabiamila ya amince da N2bn ba tare da izinin Tinubu ba? Fadar shugaban kasa ta yi martani
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya cire tallafin fetur da Dala
Shugaban kwamitin ya jaddada cewa ya zama dole gwamnati ta batar da kudin da aka adana domin yaye wahalar da mutane suka shiga.
Bola Ahmed Tinubu ya yi watsi da tsarin biyan tallafin man fetur bayan shiga ofis.
A dalilin haka, kun samu rahotanni cewa rayuwa ta kara tsada da wahala saboda yadda kudin mota ya tashi a sakamakon tsadar fetur.
Haka kuma babban bankin CBN na kasa ya daidaita farashin kudin kasar waje, matakin da aka dauka ya jawo karyewar Naira a yau.
Oyedele ya fadi yadda Tinubu ya tara kudi
Kungiyar ‘yan kasuwan ta gayyaci Oyedele ya yi jawabi, inda aka rahoto shi yana kare gwamnatin tarayya game da sakin farashin Naira.
"Mutanen Najeriya sun sadaukar da kan su a sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnati tayi; wannan ya kai N4tr a shekara.
Mun saki darajar Naira a kasuwa. Ba za a ce bai da matsala ba. Muna kuma adana wasu N4tr.
Saboda haka mun dauke kimanin N8tr daga cikin aljihun wasu mutane, mun maida su ga gwamnati."
- Taiwo Oyedele
Oyedele ya ce yanzu gwamnati za ta iya batar da wadannan kudi inda ya dace domin ceto mutane miliyan 133 da ke cikin masifar talauci.
Bola Tinubu ya saba alkawarinsa?
Sanarwa ta zo cewa ayarin shugaban kasa ba zai wuce mutane 25 a Najeriya da mutane 20 a kasar waje ba saboda a rage facaka da dukiya.
Tun yanzu, labari ya zo cewa har shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya saba alkawarin da ya dauka a ranar Talata, 9 ga watan Junairu.
Asali: Legit.ng