‘Yan Najeriya N133m ne ke Cikin Matsanancin Talauci, Gwamnatin Tarayya

‘Yan Najeriya N133m ne ke Cikin Matsanancin Talauci, Gwamnatin Tarayya

  • Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa kashi 63 na dukkan ‘yan Najeriya suna cikin matsanancin talauci tare da fatara a shekarar 2022
  • Kamar yadda binciken da MPI suka ja ragama ya nuna, mutum miliyan 133 ne ke cikin kungurmin talauci na rashi abinci, kiwon lafiya, aiki da sauransu
  • Jihar Sokoto ce ke da mafi yawan matalauta inda Ondo ke da mafi karanci duk da Buhari yace an yi binciken ne don ganowa da kawo tsarikan dakile talaucin

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa kashi 63 na mutanen dake rayuwa a Najeriya wanda yayi daidai da mutum miliyan 133 suna rayuwa cikin matsanancin talauci.

Labari da duminsa
‘Yan Najeriya N133m ne ke Cikin Matsanancin Talauci, Gwamnatin Tarayya
Asali: Original

An gabatar da wannan kiyasin ne a yayin kaddamar da binciken Nigeria’s Multidimensional Poverty Index a Abuja a ranar Alhamis.

Hukumar kula da kididdiga ta kasa tare da National Social-Nets Coordinating Office, United Nations Development Programme, United Nations Children’s Fund da Oxford Poverty and Human Development Initiative ne suka yi binciken.

Kara karanta wannan

Manyan Kudu maso Kudu Sun Fara Shirye-Shiryen Karya Bola Tinubu a Zaben 2023

Daily Trust ta rahoto cewa matakan da aka yi amfani dasu wurin binciken sun yi dogaro ne da Multidimensional Poverty Index tare da duba bangaren lafiya, yanayin rayuwa, ilimi, tsaro da rashin aikin yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Binciken wanda aka yi bayan duba gidaje 56,000 a fadin jihohi 36 na kasar nan da babban birnin tarayya, an yi shi tsakanin watan Nuwamban 2021 da Fabrairun 2022, yace kashi 65 na talakawa, mutum miliyan 86 suna rayuwa a arewa yayin da kashi 35 kusan miliyan 47 suna rayuwa ne a Kudu.

Binciken ya bayyana jihar Sokoto matsayinta jihar da tafi kowacce talauci a fadin jihohin inda take da kashi 92 yayin da jihar Ondo ke da mafi karanci da kashi 27.

A yayin jawabi a taron, shugaban kasa Muhammadu Buhari yace an dauka matakin yin wannan binciken ne saboda ya samar da hanyar ganowa da magance talauci.

Kara karanta wannan

Anyi Gwanjon Sukurkutattun Takalman Biloniya kan N96.6m

Jaridar Punch ta rahoto cewa, Buhari ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadarsa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Sama da rabin ‘yan Najeriya na cikin mawuyacin hali

Rahoton ya kara da cewa:

“Sama da rabin ‘yan Najeriya suna cikin talauci kuma suna girki ne da kashin dabbobi, itace ko gawayi a maimakon makamashi mai tsafta.
“Da yawa daga cikin abubuwan da suka dace kamar tsaftataccen muhalli, kiwon lafiya mai kyau, abinci da gidan zama duk basu da shi.
“Sai dai a baki daya lamarin, fatarar kudi tafi karanta a fadin jihohi. A Najeriya, kashi 40.1 na jama’ar kasar a 2018/2019 suna cikin talauci kuma kashi 63 suna cikin fatara ta fuskoki daban-daban kamar yadda MPI ta bayyana a 2022.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel