‘Ba Zan Lamunci Ku Ci Gaba da Kashe Mutane ba’, Tinubu Ya Kyankyasa Gargadi Ga Manyan Sojojin Kasa

‘Ba Zan Lamunci Ku Ci Gaba da Kashe Mutane ba’, Tinubu Ya Kyankyasa Gargadi Ga Manyan Sojojin Kasa

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce gazawar hafsoshin sojan kasar wajen kawo karshen rashin tsaro zai kawo cikas ga shirinsa na tattalin arziki
  • Tinubu, a lokacin da yake jawabi ga hafsoshin tsaron a fadarsa, ya ce idan har aka ci gaba da samun tabarbarewar tsaro, hakan zai shafi tattalin arzikin da gwamnatinsa ke son ginawa
  • Shugaban ya kuma yi kashedi kan harin bama-bamai da ake kaiwa jama'a bisa kuskure kamar yadda ya faru a Kaduna kwanan nan

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Aso Villa, AbujaShugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci gazawar hafsoshin sojin kasar ba a yakin da kasar ke yi da wasu matsalolin tsaro.

Kara karanta wannan

Bayan cewa bai son a kai masa ziyara, Buhari ya yi kyautar galleliyar mota ga dan a mutunsa

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da jagororin tsaro a wani taron da ya gudanar a ranar Juma’a, 5 ga watan Janairu a fadar gwamnati da ke Abuja.

Shugaban ya yi nuni da cewa, duk da cewa an samu ci gaba mai kyau wajen kawar da wasu kalubalen tsaron, amma ana iya tabbatar da nasara ne kawai ta hanyar kawo karshen kalubalen ta hanyoyi daban-daban.

Tinubu ya gargadi sojoji kan rashin tsaro
Tinubu ya ce ba zai lamunci gangancin sojoji ba | Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gazawar da sojoji suka yi wajen kawo karshen hare-haren da tsageru ke kaiwa jama’a a kasar, zai gurgunta tattalin arzikin dala tiriliyan 1 da gwamnatinsa ta yi niyyar samarwa cikin ‘yan shekaru.

Ku daina kuskuren jefa bama-bamai kan jama'a

Tinubu ya kuma yi gargadi game da yadda sojojin kasar ke sakin bama-bamai cikin kuskure kan mutanen da basu jiba basu gani ba.

Kara karanta wannan

"Babu lokacin murna" Shugaba Tinubu ya aike da zazzafan gargaɗi ga hafsoshin tsaron Najeriya

Shugaban ya bukaci hukumomin tsaro da su ci gaba da yaki da tabarbarewar tsaro a kasar, inda ya kara da cewa "gazawa ba zabi bane a karkashin jagorancina," Sahara Reporters ta tattaro.

Shugaba Tinubu, ya ci gaba da cewa, dole ne sojojin kasar su tabbatar da cewa manufarsu ita ce su taimaka wajen samar da dawwamamman tsaro.

Atiku ya magantu kan kisan ‘yan maulidi

A tun farko, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da kisan masu Maulidi a jihar Kaduna.

Atiku ya bukaci ayi kwakkwaran bincike don tabbatar da zakulo wadanda su ka aikata wannan aika-aika.

Dan takarar PDP ya bayyana haka a shafin X yayin da ya ke nuna alhini a yau Talata 5 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel