NDLEA Ta Gano Yadda Matasan Borno Ke Jika Fitsari da Kashin Kadangare Su Sha Su Yi Maye

NDLEA Ta Gano Yadda Matasan Borno Ke Jika Fitsari da Kashin Kadangare Su Sha Su Yi Maye

  • Biyo bayan tsaurara matakan hukumar NDLEA kan sha da fataucin kwayoyi, matasa a Gombe sun dauki wani salo
  • A cewar NDLEA, yanzu matasan sun koma jika fitsari ya yi kwana 10, a hada da kashin raƙumi a sha a bugu
  • Bullowar wadannan sabbin dabarun shan abun bugarwar, ya mayar da aikin hukumar baya, amma suna kokari kan hakan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Borno - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta bayyana cewa matasa a jihar Borno na jika fitsari tsawon kwana 10 don su sha su bugu.

Kwamandan muggan kwayoyi na NDLEA a jihar Borno, Iliyasu Mani, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Maiduguri a ranar Alhamis, 4 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram sun yi ajalin babban malamin addini a Yobe bayan hallaka wasu mutane 5

Matasan Borno na shan fitsari da kashin kadangare
NDLEA ta gano yadda matasan Borno ke jika fitsari da kashin kadangare su sha su yi maye. Hoto: Getty Images/STEFAN HEUNIS
Asali: Getty Images

Matasan Borno sun koma shan fitsari da kashin kadangare

The Punch ta ruwaito Iliyasu Mani na nuna damuwarsa kan yadda matasan ke yin hade-hade matsayin kwayoyi don kawai su yi maye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce yanzu sun koma hada kashin kadangare, fitsarin rakumi da sinadarin 'menthol' a lemun kwalba suna sha don su bugu.

Mani ya kara da cewa matasan na shakar warin masai da ruwan kwata duk don dai su yi marisa, tun da an hana safarar kwayoyi, a cewar rahoton The Nation.

Hade-haden da matasa ke yi don su sha su yi maye

A cewar kwamandan NDLEA:

"Bari dai na yi maku bayani kan hade-haden da suke yi, suna shan wiwi, maganin tari a hada da 'codeine'; tramol, diazafam, solisho, ruwan gam.
"Sauran kayan mayen sun hada da warin masai, ruwan kwata, kashin kadangare, rafanol, fitsarin rakumi, tsuma fitsari ya yi kwana 10, da dai sauran su."

Kara karanta wannan

"Manyan coci za su ruguje": Jerin malamai 2 da suka hangowa kiristoci matsala a 2024

Mani ya ce kokarin hukumar NDLEA na dikile sha da fataucin kwayoyi a Borno na samun koma baya samun matasan sun fara komawa ga sinadaran gargajiya.

Amma ya ce hukumar ta samar da cibiyoyin ta a jami'o'in jihar don zama cibiyar bincike kan sha da fataucin miyagun kwayoyi, da nufin dakile dabi'ar, rahoton Peoples Gazette.

Hukumar Hisbah a Kano ta cafke mota makare da kwalaben barasa

A wani labarin, hukumar Hisbah a jihar Kano ta ce ta kama wata mota dauke da kwalabe dubu 24 na barasa a hanyar Kano-Zariya, tare da kama mutum uku.

Wannan sumamen na daga cikin yunkurin hukumar na tabbatar da Shari'a a jihar Kano, tare da hana sha da fataucin barasa, a cewar daraktan Hisbah, Alhaji Abba Sufi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel