Matan aure da dalibai mata sun fi kowa shan kayan maye a Katsina – Hukumar NDLEA

Matan aure da dalibai mata sun fi kowa shan kayan maye a Katsina – Hukumar NDLEA

Rahotanni sun kawo cewa matan aure da dalibai mata sun fi kowa ta’ammali da kayan shaye-shaye a jihar Katsina.

Shugabar hukumar dake yaki da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta bayyana cewa babu wata babbar makarantar da bazaka ga dalibanta mata daga cikin masu shayeshaye ba.

A cewar ta an kama mafi akasarinsu ne a yayinda suke shaye-shayen a gefen makarantar ko kuma suna saye ko kuma suna sayarwa.

Matan aure da dalibai mata sun fi kowa shan kayan maye a Katsina – Hukumar NDLEA
Matan aure da dalibai mata sun fi kowa shan kayan maye a Katsina – Hukumar NDLEA

Sannan kuma ta kara da cewa an kama wasunsu ne a hanyar Kano inda za su je su sawo kwayoyin’ inji Maryam.

KU KARANTA KUMA: Obasanjo ya cire Buhari daga sunayen shugabannin Afrika dake kawo chanji a shugabanci

Ta kara da cewa a shekarar da ta gabata sun damke mata 50, 20 daga cikinsu yan mata ne masu kwanannan shekarun da ba su wuce shekaru 18 zuwa kasa ba da aka samu kayan mayen da suka kai nauyin 432 Kg

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: