Ku Kara Wa Tinubu Shekaru 3 Kacal, Sanatan APC Ya Fadi Gaskiya Kan Wahala a Najeriya, Ya Tura Bukata

Ku Kara Wa Tinubu Shekaru 3 Kacal, Sanatan APC Ya Fadi Gaskiya Kan Wahala a Najeriya, Ya Tura Bukata

  • Sanatan APC a jihar Abia, Orji Kalu ya bukaci 'yan Najeriya su kara wa gwamnatin Tinubu shekaru uku
  • Kalu ya ce tabbas sun san ana cikin mawuyacin hali a kasar amma Tinubu ya himmatu wurin tabbatar da inganta tattalin arzikin Najeriya
  • Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a jiya Talata 2 ga watan Janairu a karamar hukumar Afikpo ta Kudu a jihar Ebonyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Sanata Orji Uzor Kalu ya roki 'yan Najeriya karin hakuri kan halin da suke ciki a kasar.

Kalu ya bukaci karin hakuri har na tsawon shekaru uku don bai wa Shugaba Tinubu daidaita al'amuran kasar.

Kara karanta wannan

2024: Shugaba Tinubu ya bayyana babban buri ɗaya tal da ya sa ya nemi hawa mulki sau 3 a Najeriya

Sanatan APC ya roki 'yan Najeriya uzurin shekaru 3 ga Tinubu
Orji Kalu ya bukaci a kara hakuri da Tinubu a Najeriya. Hoto: Bola Tinubu, Orji Uzor Kalu.
Asali: Facebook

Mene Kalu ke cewa kan Tinubu?

Tsohon gwamnan jihar Abia ya bayyana haka ne a jiya Talata 2 ga watan Janairu a karamar hukumar Afikpo ta Kudu a jihar Ebonyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan ya ce tabbas 'yan Najeriya su na cikin wani hali amma Tinubu ya himmatu wurin tabbatar da inganta tattalin arziki.

Ya ce dole idan zaka yi dinki sai ka yayyanka yadi inda ya ce a yanzu Tinubu abin da ya dukufa a kai kenan, cewar Premium Times.

Ya ce:

"Gwamnatin APC yanzu ta na yanka yaduka ne, kafin ka yi dinki sai ka yanka yaduka, a yanzu Tinubu ya na kan yanka yadukan ne.
"Ya kamata ku bamu shekaru biyu ko uku, tabbas mun sani ana shan wahala a kasar baki daya.
"Ku bamu karin shekaru biyu don samun damar dinka yadukan sosai don su yi kyau."

Kara karanta wannan

"Manyan coci za su ruguje": Malamin addini ya yi hasashe kan 2024, ya jero masifu 4 a mulkin Tinubu

Wannan na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke cikin mawuyacin hali tun bayan cire tallafin mai a kasar, Daily Post ta tattaro.

A bangarenshi kuma, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana ji dadinsa kan cire tallafin mai da Shugaba Tinubu ya yi a watan Mayun 2023.

Buhari ya ce ya yi tsammanin hakan zai rage yawan ziyara da mutane ke kai masa a gidansa da ke Daura a jihar Katsina.

Tinubu ya yi wa 'yan kasa babban alkawari

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin inganta harkar wutar lantarki a shekarar 2024 da aka shiga.

Tinubu ya ce ya sanya hannu a yarjejeniya da kamfanin Siemens da ke Jamus don inganta wutar a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel