Fitaccen Malamin Addini Ya Bayyana Babbar Matsalar da Za a Samu Kafin Samun Daidaito a 2024, Ya Koka

Fitaccen Malamin Addini Ya Bayyana Babbar Matsalar da Za a Samu Kafin Samun Daidaito a 2024, Ya Koka

  • Shahararren Fasto a Najeriya, Enoch Adeboye ya yi hasashen abubuwan da za su faru a sabuwar shekarar 2024
  • Adeboye ya ce tabbas abubuwa za su rikice a shiga mummunan yanayi amma daga bisani komai zai daidaita
  • Faston ya bayyana haka a daren jiya Lahadi 31 ga watan Disamba a yayin bikin sabuwar shekarar 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas – Fitaccen Fasto a Najeriya, Enoch Adeboye ya bayyana cewa komai zai daidaita kafin samun sauki a 2024.

Adeboye wanda shi ne shugaban cocin ‘Redeemed Christian Church of God’ ya bayyana haka ne yayin hasashen sabuwar shekarar 2024.

Malamin addini ya yi hasashen abubuwan da za su faru a shekarar 2024
Fasto Adeboye ya yi magana kan sabuwar shekarar 2024. Hoto: Enoch Adeboye.
Asali: Facebook

Mene Adeboye ke cewa kan shekarar 2024?

Faston ya ce tabbas abubuwa za su rikice a shiga mummunan yanayi amma daga bisani komai zai daidaita, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Atiku ya fadi matsala 1 da ta wajaba Shugaba Tinubu ya shawo kan ta a shekarar 2024

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Enoch ya bayyana haka a daren jiya Lahadi 31 ga watan Disamba a yayin bikin sabuwar shekarar 2024.

Ya ce duk abin da Ubangiji ke fada ya fade su ne cikin wasu kalmomi kuma addu’a za ta taimaka a 2024.

Ya ce:

“Abubuwa za su sake lalacewa kafin komai ya daidaita, tabbas za su kara kamari kafin daga bisani su dawo dai-dai.”
Faston ya bukaci ‘yan Najeriya da su dage da addu’a inda ya ce akwai damarmaki da za su samu da dama a sabuwa shekarar 2024.

Karin matsaloli a shekarar 2024

Ya ce saboda iska ta na hurawa shi ya ke tabbatar da cewa abubuwa za su daidaita a sabuwar shekarar da za a shiga, Vanguard ta tattaro.

Ya kara da cewa:

“Wasu mutane za su fara a matsayin marasa galihu amma za su zama wadanda ake ji da su zuwa tsakiyar shekarar.”

Kara karanta wannan

"Manyan coci za su ruguje": Malamin addini ya yi hasashe kan 2024, ya jero masifu 4 a mulkin Tinubu

Adeboye ya kara da cewa a matakin kasa da kasa za a samu matsalolin cututtuka kamar cutar daji da ciwon sukari da kuma hawan jini.

Fasto ya hasashen abin da zai faru a 2024

A wani labarin, Shahararren Fasto, Philip Goodman ya bayyana abubuwan alkairi da za su faru a sabuwar shekarar 2024.

Faston ya ce daga cikin abubuwan da za su faru akwai karyewar farashin man fetur a kasar inda zai zube warwas.

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen shiga sabuwar shekara da ake tsammanin samun sauki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.