Innalillahi: Ƴan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Ana Shirin Taron Addini a Arewa, Sun Kashe Sama da 15

Innalillahi: Ƴan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Ana Shirin Taron Addini a Arewa, Sun Kashe Sama da 15

  • Mutanen da ba su gaza 16 sun rasa rayukansu a wani sabon harin ƴan ta'adda a kauyen Mushu da ke jihar Filato
  • Rundunar sojin haɗin guiwa ta Operation Save Haven ta tabbatar da kai harin ranar Asabar kuma ta ɗauki mataki
  • Gwamna Celeb Mutfwang ya yi tir da kai harin kuma ya umarci jami'an tsaro su gaggauta kamo duk mai hannu kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Yayin da ake shirin bukukuwan kirsimeti, ƴan bindiga sun halaka mutane aƙalla 16 a sabon harin da suka kai ƙauyen Mushu, ƙaramar hukumar Bokkos a jihar Filato.

Mai magana da yawun Operation Safe Haven, rundunar sojin haɗim guiwa mai aikin wanzar da zaman lafiya a jihar, Kaftin James Oya ne ya tabbatar da haka ga Premium Times.

Kara karanta wannan

Ana ta shirin yanke hukunci, Kanawa sun yi wa Abba Gida-Gida babbar tarba a jihar Kano

Gwamnan Celeb Mutfwang na jihar Filato.
Mutane 16 Sun Mutu a Sabon Harin Yan Bindiga a Jihar Filato Hoto: Celeb Mutfwang
Asali: Facebook

A cewar Kaftin James, maharan sun kai wannan hari kauyen ne ranar Asabar a daidai lokacin da mutane suka kwanta bacci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa:

"Biyo bayan samun labarin kai harin, an kara girke jami'an tsaro cikin shirin ko ta kwana a yankin domin dakile duk wani yunƙuri na karya doka da oda."
"An samu tashin hatsaniya bayan kai harin amma zuwa yanzun jami'an tsaro sun shawo kan lamarin."

Gwamna Mutfwang ya yi tir da harin

Gwamna Caleb Mutfwang ya yi Allah-wadai da harin wanda ya yi ajalin rayuka, yana mai bayyana harin a matsayin dabbanci da kuma rashin tausayi.

A wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran gwamnan, Gyang Bere, ya fitar, Mutfwang ya umarci hukumomin tsaro su gaggauta kamo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aikin.

Mista Bere ya ce gwamnan ya nuna matukar damuwarsa kan lamarin, inda ya bukaci al’ummar jihar da su sanya ido, kana su kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga jami’an tsaro domin daukar mataki cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da shirin Kirsimeti, 'yan bindiga sun sheke gomman mutane a jihar Filato

Ya kuma nuna rashin daɗinsa kan yadda ire-iren waɗannan maharan ke cutar da mutane da lalata dukiyoyi ba tare da sun fuskanci hukunci ba., cewar Daily Trust.

Yan sanda sun samu nasara a jihar Katsina

A wani rahoton na daban Dakarun ƴan sanda sun kai samame maɓoyar ƴan ta'adda kuma sun daƙile mummunan nufinsu a kauyen Yargoje a jihar Katsina.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel