“Ni Matsafiya Ce”: Malamar Addini Ga Mabiyanta, Tace Yana Cikin Littafi Mai Tsarki
- Babbar fasto Francisca Emmanuel ta majami'ar 'Transformation World Ministries' ta ayyana kanta a matsayin matsafiya, tana mai bayyana cewa yana cikin littafi mai tsarki
- Fasto Emmanuel ta kafa hujjar cewa ba za a iya cin nasarar wasu fadace-fadacen da addu'a ba kawai sannan tace akwai bukatar ayi amfani da tsafi don shawo kan mutanen boye
- Malamar addinin ta jaddada cewar zama matsafi na da matukar muhimmanci don mayar da mugayen asiran da ake turawa mutum da lallasa makiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Francisca Emmanuel, wata babbar fasto a majami'ar 'Transformation World Ministries', ta ayyana cewar ita matsafiya ce.
A wa'azinta na baya-bayan nan, Fasto Emmanuel ta yi ikirarin cewa yana cikin littafi mai tsarki mutum ya zama matsafi maimakon dukawa da yin addu'a kawai, rahoton Punch.
Kana bukatar abun da ya fi adduna - Fasto Emmanuel
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamar addinin ta kuma bayyana cewa mutum na bukatar abun da ya fi addu'a don shawo kan matsaloli da shan kan mutanen boye da ke kawo tangarda ga rayuwar mutum.
Kalamanta:
"Ni matsafiya ce ban san yadda kake son tunani a kansa ba saboda idan ka shiga gonata zan sanya maka 'Allah ya ji kanka' maimakon kai ka saka mun."
A cewarta, akwai yaki da dama da basa bukatar addu'o'i kawai face tsafi don shawo kansu.
Ta ce:
"A matsayinka na Kirista, kana bukatar zama matsafi don idan makiyinka ya yi maka abu mara kyau, zai koma kansa. Idan suka jefo maka wani abu, zai koma kansu.
"Akwai fadace-fadacen da sai ka zama matsafi don shawo kansu. Baya bukatar mutum ya durkusa kawai, ko ya zauna da yin magana. Duk abun da kake yi akasin shi makiyinka ke yi. Kana bukatar tsafi don maganin makiyinka da samun hutu."
Da take jaddada cewar tsafi na littafi mai tsarki, Emmanuel ta ce:
"Kada ka bari kowa ya yaudareka. Tsafi na littafi mai tsari. Kasancewa matsafi na littafi mai tsarki.
Yan Najeriya sun yi martani
Rene Prism ta bayyana a Facebook:
"Idan mutum ya ce maka abu na a littafi mai tsarki, hakan na nufin yana rubuce a cikin littafi mai tsarki. Yana cikin littafi mai tsarki baya nufin Allah ya amince da shi, yana iya kasance gargadi da bayanin hukuncin da zai biyo baya idan ka aikata shi."
Olajide Afolabi ya ce:
"Tana magana ne daga tsohon littafi, ya kamata a fada mata cewa yanzu bama bukatar aikata hakan kuma, Yesu ya yi amfani da jininsa saboda wanke zunubanmu."
Babatunde Gabriel ya ce:
"Mutane da dama sun yi shiru, ina tunanin, da ace wannan ya zo daga cocin masu sanya fararen kaya ne. Allah ya kare Kiristocin Najeriya."
Enuechie Cletus ya ce:
"Bana a matsayin yanke mata hukunci amma ina rokon Allah ya yafe mata."
Buhun shinkafar zai koma 80k, Fasto
A wani labari na daban, kamar yadda ya saba bisa al'ada, shugaban cocin INRI Spiritual, Primate Babatunde Elijah Ayodele (JP), ya saki sakonninsa game da shekarar 2024.
A hasashensa, malamin addinin ya bayyana cewa farashin shinkafa yar waje zai yi tashin gwauron zabi uwa N80,000 kan kowani buhu daya a kasar.
Asali: Legit.ng