Sabuwar kungiyar masu wa'azi ta billo a jihar Sokoto

Sabuwar kungiyar masu wa'azi ta billo a jihar Sokoto

Labarin da muke samu ya nuna cewa wata sabuwar kungiya ta masu ikirarin wa'azin musulunci dauke da miyagun makamai, ta bulla a cikin jihar Sakoto daga jamhuriyyar Nijar mai makwabtaka da kasar.

Shafin BBC Hausa ta ruwaito cewa ana zargin tun a watanni biyu da suka gabata ne 'ya'yan kungiyar suka soma bula a wasu garuruwa na yankin karamar hukumar Tangaza.

Bisa ga wani majiya da ya nemi a sakaya sunansa ya ce 'ya'yan kungiyar na bin kauyuka suna karbar zakka daga masu hannu da shuni, kuma suna yin bulala ga mutanen da suka aikata abubuwan assha da suka saba wa dokokin addinin musulunci.

Sabuwar kungiyar masu wa'azi ta billo a jihar Sokoto
Sabuwar kungiyar masu wa'azi ta billo a jihar Sokoto
Asali: Depositphotos

Ya kuma shaida cewa 'yan kungiyar sun fi mutum 200, kuma cikinsu akwai fulani da turawa da larabawa dauke da rawani da bindigogi.

''Suna bin gida-gida don karba kudade mai rago zai bada naira dari biyu mai kiwon sa kuma zai ba da naira dari biyar''.

Mutumin ya kuma shaida cewa suna kai yara cikin daji, suna koya musu wasu abubuwa, idan za su dawo da su zai su basu babur.

KU KARANTA KUMA: Wadanda suka sauya sheka daga APC sun yi danasanin marawa Buhari baya a 2015

Yankin Tangaza a jihar Sokoto na makwabtaka da jamhuriyar Nijar inda ake zargin 'yan sabuwar kungiyar da shigo wa.

Wannan al'amari dai na haifar da barazanar tsaro a yankin, kuma zuwa yanzu jami'an tsaro ba su tabbatar da wannan labarin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng