Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Allah Ya Yi Wa Fitaccen Jarumin Shirin Fim Rasuwa

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Allah Ya Yi Wa Fitaccen Jarumin Shirin Fim Rasuwa

  • Fitaccen jarumi a masana'antar shirya fina-finai ta kudancin Najeriya, Nollywood, Dejumo Lewis, ya mutu yana da shekara 80 a duniya
  • Jarumi Saidi Balogun ne ya sanar wannan rasuwa ranar Asabar, 23 ga watan Disamba, 2023 a dandalin sada zumunta
  • Masoyan marigayi jarumin sun garzaya shafukan sada zumunta suna jimami tare da rubuta kalaman bankwana da mamacin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Shahararren jarumi a masana'antar shirya fina-finan turanci, Nollywood da ke kudancin Najeriya, Dejumo Lewis, ya riga mu gidan gaskiya.

Fitaccen jarumin ya rasu ne yana da shekaru 80 a duniya bayan fama da wata rashin lafiya da ba a bayyana ba kawo yanzu.

Dejumo Lewis ya rasu.
Fitaccen Jarumin Nollywood Ta Kudancin Najeriya, Lewis Ya Kwanta Dama Hoto: @olorisugergal
Asali: Instagram

Abokin aikinsa a masana'antar shirya fim, jarumi Saidi Balogun, shi ne ya sanar da rasuwar fitaccen jarumin a shafinsa na Intagram.

Kara karanta wannan

Yan sandan Kano sun kama tubabben dan fashi da makami, suna neman wasu 72 ruwa a jallo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanarwan da ya wallafa yau ranar Asabar, 23 ga watan Disamba, 2023, jarumi Balogun ya rubuta, "Mu kwana lafiya Dejumo Lewis."

Haka nan kuma jarumin ya yi wa mamacin fatan samun salama a rayuwa ta gaba da zai yi a barzahu.

Sai dai har kawo yanzu da muke tattara wannan rahoton, babu wani cikakken bayani kan abin da ya yi sanadin rasuwarsa.

Fina-finan da margayi Lewis ta taka rawa a ciki

Marigayin ya taka rawa da fina-finai da dama kamar irin su, "A place in the Stars," da kuma, "Crossroad."

Bugu da ƙari, Margayi Lewis ya fito a matsayin Sarki, "Oloja na Oja" a kayataccen shirin nan mai dogon zango, "Village Headmaster" wanda aka jima ana haska shi a NTA.

Masoya da masu fatan alheri sun jajanta tare da jimamin wannan rashi a kafafen sada zumunta. Haka nan kuma sun yi masa addu'ar samun salama a bayan mutuwa.

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya yayin da jami'in soja ya mutu a hanyarsa ta zuwa daurin aurensa

Yan sanda sun ragargaji yan bindiga a Katsina

A wani rahoton na daban Yan bindiga sun ga takansu yayin da dakarun yan sanda suka far musu a yankin ƙaramar hukumar Kankara ta jihar Katsina

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel