Innalillahi: Fitacciyar Jarumar Fina-finai Ta Tsallake Rijiya Ta Baya, Ta Yi Godiya Ga Allah

Innalillahi: Fitacciyar Jarumar Fina-finai Ta Tsallake Rijiya Ta Baya, Ta Yi Godiya Ga Allah

  • Mercy Aigbe, shahararriyar jarumar fina-finan Nollywood ta sha da kyar bayan motarta ta gamu da wani mummunan hatsari
  • Mercy ta wallafa bidiyon a shafinta na Instagram bayan ta tsira inda ta ce tayar motar ta fashe ta na tsakiya da gudu mai tsanani
  • Lamarin ya faru ne a yau Asabar 23 ga watan Disamba a kan hanyarta ta zuwa Legas daga jihar Edo inda tayar motar ta yi bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Mercy Aigbe ta tsallake rijiya ta baya a wani mummunan hatsarin mota.

Lamarin ya faru ne a yau Asabar 23 ga watan Disamba a kan hanyarta ta zuwa Legas daga jihar Edo, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta saki sunayen 'yan Najeriya da za ta ba tallafin N50k a 2024

Fitacciyar jarumar fina-finai ta yi hatsarin mota, da kyar ta sha
Fitacciyar jarumar fina-finai, Mercy Aigbe ta gamu da tsautsayi. Hoto: @mercyaigbe.
Asali: Instagram

Yaushe hatsarin motar ya afku da jarumar?

Mummunan hatsarin motar ya afku bayan tayar motar ta fashe lokacin da ta ke tsaka da mummunan gudu a kan hanya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aigbe ta ce ta na kan hanyarta ne ta zuwa Legas don tallata wani sabon fim da ta yi mai suna 'Ada Omo Daddy'.

Jarumar ta wallafa faifan bidiyon a shafin Instagram inda ta ce wannan shi ne babban bala'in da ta taba cin karo da shi mafi tsoro a rayuwarta.

Wane martani Mercy ta yi?

Mercy ta godewa ubangiji wanda ya kare rayuwata daga salwanta inda ta haɗa da wata wakar Kiristanci a faifan bidiyon.

Mutane da dama sun yi martani bayan jarumar ta wallafa faifan bidiyon a shafinta na Instagram jim kadan bayan afkuwar lamarin.

Jama'a da dama sun jajanta mata inda su ka ce hakan wani ikon Allah ne da ya kare ta daga iftila'in.

Kara karanta wannan

Masanin tattalin arziki ya yi jasashen abin da zai faru da Najeriya a shekarar 2024

Mercy ta fadi dalilin shigarta Musulunci

A wani labarin, Mercy Aigbe ta bayyana dalilin shigarta addinin Musulunci wanda har yanzu ta ke jin dadi a rayuwarta.

Aigbe ta ce musabbabin sauya addininta daga Kiristanci zuwa Musulunci shi ne soyayya wanda ta ci karo da ita bayan haduwarta da mijinta.

Jarumar fina-finan Nollywood ta kara da cewa ta fuskanci kalubale da dama yayin soyayyar tasu da mijinta wanda ya nuna mata tsantsar kauna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel