An Kama Wani Mutum Kan Kashe Matarsa Saboda Ta Ki Dafa Abincin da Ya Fi So
- Wani abun bakin ciki ya afku a yankin Olota da ke karamar hukumar Alimosho ta jihar Lagas lokacin da wani mutum ya kashe matarsa saboda ta ki girka abincin da ya fi so
- Jami'an yan sandan sun kama mijin bayan kanin marigayiyar ya kai rahoton lamarin
- Wata majiya ta yan sanda ta bayyana cewa an tura lamarin zuwa sashin binciken laifi na jiha da ke Panti
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Alimosho, jihar Lagos - Jami'an yan sanda sun kama wani magidanci kan zargin kashe matarsa saboda ta ki girka abincin da ya fi so a yankin Olota da ke karamar hukumar Alimosho ta jihar Lagas.
Mummunan al'amarin ya afku ne a ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba, lokacin da mijin ya dawo daga wajen aiki sannan ya ga cewa matar ta girka taliya ne ba abincin da ya fi so ba, rahoton Punch.
An tattaro cewa matar ta ce ga garinku ne a hanyar kai ta asibiti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya a ofishin yan sanda na yankin Meiran, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce an kama wanda ake zargin ne bayan dan uwan marigayiyar ya kai rahoton lamarin ofishin yan sanda.
Majiyar ta ce:
"Dan uwan marigayiyar ne ya zo ya kawo rahoton lamarin. Ya ce mijin ya kashe yar'uwarsa.
"Sai dai kuma, babu wanda ya fito ya fada mana cewa mijin ne ya kashe ta. Mun kama mijin. Tuni muka tura lamarin zuwa sashin binciken laifuka na jihar, Panti."
An kama magidanci kan kashe matarsa
A wani labari makamancin wannan, Legit Hausa ta kawo a baya cewa jami'an rundunar yan sandan jihar Ekiti sun kama wani fasto, Abiodun Sunday kan zargin kisan matarsa, Tosin Oluwadare.
Kakakin yan sandan jihar, DSP Sunday Abutu, ya ce mummunan al'amarin ya afku ne a yankin Ido-Ile da ke karamar hukumar Ekiti ta Yamma a jihar.
An yi caraf da magidancin ne bayan ya yi wa matar tasa dukan tsiya da taɓarya da niyyar salwantar da ranta a ranar 2, ga watan Disamban 2023.
Asali: Legit.ng