Tudun Biri: Gwamnonin Arewa Sun Hadu a Kaduna, Karin Bayani Kan Abin Da Za Su Tattauna

Tudun Biri: Gwamnonin Arewa Sun Hadu a Kaduna, Karin Bayani Kan Abin Da Za Su Tattauna

  • Rahotanni na nuni da cewa gwamnonin jihohin Arewa sun shiga wata ganawa a jihar Kaduna don tattauna batun tsaro da tattalin arzikin shiyyar
  • Wannan ganawar ita ce ta farko da gwamnonin suka yi tun bayan da suka kama aiki a watan Mayun shekarar 2023
  • Haka zalika ana sa ran gwamnoni za su yi amfani da damar wajen tattauna batu kan harin da sojoji suka kai a wani kauyen jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kaduna - Gwamnoni 19 na jihohin Arewa ne aka ruwaito sun hadu a jihar Kaduna a yau Juma'a don tattauna batutuwan da suka shafi harin da sojoji suka kai kauyen jihar.

Wannan shi ne taron farko da kungiyar gwamnonin Arewa ta yi tun bayan shigarsu ofis a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tabbatar da barin Ciyamomi 21 da Kansiloli 239 ofisoshinsu, ya fadi dalili

Gwamnonin Arewa sun hadu a Kaduna
Gwamnonin Arewa sun hadu a Kaduna don tattauna batu kan matsalolin tsaro da tattalin zariki na shiyyar. Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

Channels TV ta ruwaito cewa daga cikin abubuwan da gwamnonin za su tattauna, akwai batun tsaro da kuma matsalolin tattalin arziki da ke addabar shiyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnoni 6 ba su samu damar halartar taron ba

Haka zalika, gwamnonin za su yi amfani da wannan damar wajen mika sakon ta'aziyya da jaje ga gwamnatin Kaduna kan harin bam a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar.

An ruwaito cewa gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, da takwaransa na Zamfara, Dauda Lawal da na jihar Borno, Babagana Zulum, na daga cikin mahalarta taron.

Sai dai gwamnoni shida da mataimakan gwamnoni shida cikin 19 na jihohin Arewa ba su samu halartar taron ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Gwamna Radda ya dauki malamai 7,325 aiki a jihar Katsina

A wani labarin, gwamnan jihar Katsina, Dr. Umaru Dikko Radda, ya mika takardun kama aiki ga malamai 7,325 a jihar, wadanda za su fara aiki 16 ga watan Janairun 2024.

Kara karanta wannan

Wike Vs Fubara: Karin kwamishinoni biyu sun yi murabus a jihar Rivers, adadin ya kai 6 yanzu

Gwamna Radda wanda ya yi masu nasiha kan rikon gaskiya yayin gudanar da aikin su, ya kuma yi alkawarin ba su duk wani horo da suke bukata kafin fara aiki, Legit Hausa ta ruwaito.

Gwamnan ya kara da cewa ma'aikatar ilimi na samun sauye-sauye a jihar, don haka akwai bukatar sabbin malaman su zage damtse don bunkasa harkar ilimin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.