Abdulaziz Yari ya bayyana gaskiyar lamari game da batun sauya shekarsa daga APC zuwa PDP

Abdulaziz Yari ya bayyana gaskiyar lamari game da batun sauya shekarsa daga APC zuwa PDP

  • Tsagin tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari na APC ya magantu a kan rahotannin cewa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP
  • Yari ta bakin kakakinsa, Ibrahim Magaji, ya ce har yanzu basu sauya sheka zuwa PDP ba suna dai kan tattaunawa da jam’iyyu da dama
  • Ya bayyana cewa shugaban PDP a Zamfara, Kanal Bala Mande, ya yi gaggawa wajen sanar da ficewarsu daga jam’iyyar mai mulki

Zamfara - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya bayyana rahoton sauya shekar tsaginsa zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin take gaskiya.

A ranar Lahadi ne shugaban PDP a jihar, Kanal Bala Mande mai ritaya, ya fada ma manema labarai a Gusau cewa Yari, Sanata Marafa da sauran jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun sauya sheka zuwa jam’iyyar adawar.

Kara karanta wannan

Marafa ya ragargaji APC, amma ya karyata rade-radin sauya-sheka zuwa Jam’iyyar PDP

Abdulaziz Yari ya bayyana gaskiyar lamari game da batun sauya shekarsa daga APC zuwa PDP
Abdulaziz Yari ya bayyana gaskiyar lamari game da batun sauya shekarsa daga APC zuwa PDP Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Kakakin tsagin Yari na APC, Ibrahim Magaji, ya ce shugaban na PDP a jihar ya yi gaggawa wajen sanar da batun, jaridar The Guardian ta rahoto.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Bisa ga hukuncinmu na barin APC, mun shiga tattaunawa da jam’iyyun siyasa da dama, ciki harda PDP, amma ba mu cimma matsaya da kowace jam’iyya ba.”

Marafa ya ragargaji APC, amma ya karyata rade-radin sauya-sheka zuwa Jam’iyyar PDP

A bangare guda, mun ji cewa a karshen makon da ya wuce ne aka ji Sanata Kabiru Marafa ya yi watsi da jam’iyyar APC mai mulki, ya shiga PDP, hakan ba ta tabbata ba.

A wata hira da ya yi da jaridar Tambari Hausa TV, Kabiru Marafa ya karyata wannan labari, ya ce kawo yanzu bai sauya-sheka daga jam’iyyar APC ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yari da Marafa sun sauya sheka daga APC zuwa PDP

A wannan tattaunawa da aka yi da shi, tsohon Sanatan na jihar Zamfara ya kira abin da tsofaffin shugabannin APC suka yi masu da ‘rashin hankali’.

Yari da Marafa sun sauya sheka daga APC zuwa PDP

A baya mun kawo cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Garba marafa sun sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Shugaban jam’iyyar adawa ta PDP a jihar, Ritaya kanal Bala Mande, ne ya sanar da hakan jim kadan bayan gama wani taron masu ruwa da tsaki a Gusau, babbar birnin jihar a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu.

Mande ya bayyana cewa sun zauna sannan sun yanke shawara kan batun sauya shekar Yari da Marafa sannan sun cimma yarjejeniyar aiki don ci gaban jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel