Kungiyar Izalatul bidi'a wa iqamatus Sunnah: kafuwar ta zuwa yanzu

Kungiyar Izalatul bidi'a wa iqamatus Sunnah: kafuwar ta zuwa yanzu

- Shekaru kusan 40 da su ka wuce aka kafa Kungiyar Izala

- Sheikh Ismail Idris Zakariya ne yayi wannan aiki

- A lokacin Malamin yana ganin cewa bidi'a tayi yawa a Najeriya

A shekarar 1978 ne aka kafa Kungiyar Kungiyar Jama'atul Izalatul bidi'a wa iqamatus Sunnah domin yaki da bidi'a (watau kagaggun al'amura cikin adddini) da kuma jaddada Sunnar Manzon Allah SAW.

Kungiyar Izalatul bidi'a wa iqamatus Sunnah: kafuwar ta zuwa yanzu
Malaman Kungiyar Izalatul bidi'a wa iqamatus Sunnah

Wani Kyaftin din Soja ne mai suna Sheikh Ismail Idris Zakariya Dalibi na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi wanda ya rika koyar da Jama'a riko da Hadisan Manzon Allah wanda aka ga kamar ya ci karo da koyarwar Malaman Darika na Sufaye.

KU KARANTA : Yaki na nema ya barke tsakanin manyan kasashe biyu

Kungiyar Izalatul bidi'a wa iqamatus Sunnah: kafuwar ta zuwa yanzu
'Yan agajin Kungiyar Izala na kasa

Tun a gidan Soja aka rika rikici da wannan matashi Ismail Idris wanda har aka kai ya bar gidan Soja ya kafa wannan Kungiya da niyyar yakar bidi'o'i irin wanda Shehu Usman Danfodio ya yaka shekarun baya irin su taron suna, amfani da laya, da aiki da malaman duba na tsibbu.

Kungiyar Izalatul bidi'a wa iqamatus Sunnah: kafuwar ta zuwa yanzu
Shugaban Kungiyar Izala da Shugaban kasa

Malaman Darika dai sun dauki wannan a matsayin fito na fito don haka su ka tashi da Almajiran su haikan wajen maida martani yayin da ake cewa wasu daga cikin su ma dai ba Musulmai bane gaba daya.

Kungiyar dai ta gamu da rikicin siyasa wanda har ya kai ga rabuwar wurin ibada. Kawo yanzu dai Izala tana cikin manyan Kungiyoyin da ke da ta cewa a harkar Musulunci.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Fafutukar Biyafara zuwa yanzu [Bidiyo]

Asali: Legit.ng

Online view pixel