Gwamnatin Tarayya ba za ta bari a shigo da shinkafa, kwai, nama, mai, dsr ba

Gwamnatin Tarayya ba za ta bari a shigo da shinkafa, kwai, nama, mai, dsr ba

- Gwamnatin Tarayya ta bude wasu daga cikin iyakokin kasan Najeriya jiya

- Daga yanzu dai za a koma shiga da fita da kaya ta iyakokin tudun kasar

- Har gobe bai halatta a shigo da shinkafa da tsofaffin gwanjon motoci ba

A jiya shugaba Muhammadu Buhari ya amince da bude wasu daga cikin iyakokin kasan Najeriya. Iyakokin sune na: Illela, Maigatari, Seme da kuma Mfun.

Da wannan mataki da aka dauka, za a koma shigo da fita da kaya ta iyakokin ba tare da bata lokaci ba, bayan an garkame iyakokin kasan tun cikin 2019.

Duk da sake bude iyakokin, akwai wasu kayan da gwamnatin tarayya ba ta yarda a shigo da su ba.

Kamar yadda Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar 17 ga watan Disamba, 2020, kayan da aka haramta shigowarsu ta iyakokin sun hada har da shinkafa.

KU KARANTA: Buhari ya ce a bude wasu iyakokin kan tudu

Kamar yadda Ministar tattalin arziki, Zainab Ahmed ta yi jawabi, jami’an kwastam ba za su bari a shigo da shinkafa, da wasu kayan abinci irinsu man girki ba.

Haka zalika bai halatta a shigo da mai har kamar Mayonnaise ba. Sauran abubuwan da aka haramta su ne: Tsuntsu (matacce ko kuma mai rai) da kuma kwai.

Kwan da aka halasta shigowa da shi cikin Najeriya shi ne na kyankyasa. Sai kuma naman alade da saniya. Sukari, taliya (har da Indomie) ba su halatta ba.

Ragowar abubuwan da aka hana shigo da su sun hada da kwayar maganin Paracetamol, darduma da kayan sutura, gwanjon motocin da su ka haura shekara 15.

Gwamnatin Tarayya ba za ta bari a shigo da shinkafa, kwai, nama, mai, dsr ba
Buhari da wani Jami'in Kwastam Hoto: www.pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnati za ta jawo layin gas daga Ajaokuta zuwa Kaduna da Kano

Tsinken sakace ya na cikin rukunin su shinkafa, shi ma bai halasta a shigo da shi ta iyakokin kasa ba.

A jiya kun ji cewa Majalisar kula da cin abinci mai lafiya a Najeriya ta amince da wani tsari na shekara biyar da aka fito da shi domin maganin yunwa a kasar nan.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa ana sa ran wannan dabaru da gwamnati ta zo da shi zai taimaka wajen yaki da matsalar samun abinci mai lafiya.

Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin Tarayya za ta dabbaka wannan manufa tsakanin 2021-2025.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng