Matashi Ya Kona Satifiket Daga Firamare Har Jami’a Bayan Shafe Shekaru 13 Ba Aiki, Ya Ba da Shawara

Matashi Ya Kona Satifiket Daga Firamare Har Jami’a Bayan Shafe Shekaru 13 Ba Aiki, Ya Ba da Shawara

  • Wani matashi da ya kammala karatun digiri ya bayyana rashin jin dadinshi kan yadda ya kammala karatu ba aiki
  • Matashin mai suna Lanre Alvin Olutimain ya ce ya kammala karatun da bautar kasa tun shekarar 2013 amma har yau shiru
  • Ya ce ya lura takardun basu da amfani shi yasa ya cinna musu wuta don ya zama izina ga ‘yan baya kada su bata lokacinsu

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Wani matashi a Najeriya da ya kamala karatun digiri ya kona dukkan satifiket da ya mallaka yayin karatu.

Fusataccen matashin ya kona satifiket din ne tun daga firamare har zuwa Jami’ar bayan shafe shekaru 13 babu aikin yi, Legit ta tattaro.

Matashi ya kona dukkan satifiket din shi tun daga firamare har Jami'a
Matashin ya bayyana dalilinshi na daukar wannan mataki. Hoto: @perfectskones.
Asali: Twitter

A wani faifan bidiyo da aka wallafa, matashin ya ce basu da amfani a wurinshi tun bayan da ya kamala karatun da kuma bautar kasa.

Kara karanta wannan

'Ku yi hakuri', MTN ya yi martani kan yafe basukan a layukan jama'a, ya fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashin mai suna Olutimain Alvin Lanre ya kamala karatun digiri a Jami’ar Ajayi Crowther da ke jihar Ogun da bautar kasa a shekarar 2013.

Lanre ya koka kan yadda duk ayyukan da ya ke nema ba ya dace inda ya ce dukkansu wanda basu yi makaranta ba ne ke yinsu, kenan takardun ba su da amfani.

Lanre har ila yau, ya shawarci matasa su koyi sana’a madadin bata lokacinsu neman satifiket da ba za su yi amfani da su ba.

Ya fitar da dukkan takardun tare da cinna musu wuta inda ya ce tun da basu da amfani tun bayan samunsu.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Mutane da dama sun yi martani kan wannan mataki na matashin:

@SAMBLINQZ:

“Idan ya yi haka, ta yaya sakonshi zai isa inda yake so.”

Kara karanta wannan

Kano: Kotun musulunci ta umurci magidanci ya karbi ɗan da ya ke kokwanton ba nasa bane

@therealmifo:

“Wannan takardun bogi ne, waye kake yaudara a nan.”

@HarunaNuhu:

“Wannan ya na da hujja sai dai bai kamata ya yi haka ba.”

@OkonkwoJohns1:

“Ya na bayyana rashin jin dadinsa a matsayin dan Najeriya.”

Farfesa ya koma wanzanci a Najeriya

A wani labarin, wani Farfesa da ke koyarwa a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsin-Ma ya cire girman kai inda ya ke hadawa da sana’ar wanzanci.

Farfesa Bashir Aliyu ya ce ya rike sana’arshi ta wanzanci tun lokacin da aka shafe watanni ana yajin aiki ba tare da biyan albashi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel