Zaben Gwamnan Imo Na 2023: Yar Yi Wa Kasa Hidima Dauke da BVAS da Sakamakon Zabe Ta Bace

Zaben Gwamnan Imo Na 2023: Yar Yi Wa Kasa Hidima Dauke da BVAS da Sakamakon Zabe Ta Bace

  • Wata 'yar bautar kasa ta bata da sakamakon zabe da kuma na'urar tantancewa a jihar Imo
  • 'Yar bautar kasar ta yi aikin wucin gadi da hukumar zabe ta INEC a karamar hukumar Mbaitoli da ke jihar
  • Wannan na zuwa ne bayan sanar da Hope Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Imo - An nemi 'yar bauta kasa wacce ta yi aikin wucin gadi a zaben gwamna an rasa a jihar Imo, Legit ta tattaro.

'Yar Bautar kasar ta yi aiki ne a karamar hukumar Mbaitoli da ke jihar inda ta gudu da sakamakon zaben da kuma na'urar tantancewa.

Kara karanta wannan

INEC ta dage tattara sakamakon zaben gwamnan Bayelsa, cikakken bayani ya bayyana

Baturen zabe a karamar hukumar Dakta Bolaji Olaleye ya ce an yi ta kiran wayarta amma ba ta amsa ba.

Ya ce watakila wani mummunan abu ya faru da ita yayin da ta ke gudanar da aikin zaben, cewar Punch.

Olaleye ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ban san meye ya faru da 'yar bautar kasar ba amma sakamakon zabe da na'urar tantancewa na tare da ita.
"Hakan ya saka aka kashe zabe a wasu mazabu 3 da ke karamar hukumar Mbaitoli."

Wannan na zuwa ne yayin da hukumar zabe ta bayyana Hope Uzodinma na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel