Cibiyar Samar da Wutan Lantarkin Najeriya Ta Sake Durkushewa a Karo Na Uku

Cibiyar Samar da Wutan Lantarkin Najeriya Ta Sake Durkushewa a Karo Na Uku

  • A yayin da gwamnati ke kokarin ganin ta dawo da martabar wutar lantarki a Najeriya, cibiyar samar da wutar ta durkushe karo na uku
  • Ko a cikin watan Satumba, sai da ta durkushe sau biyu, lamarin da aka kasa jin ta bakin hukumar TCN kan abin dake jawo irin hakan
  • Haka zalika, an samu rahoton yadda wasu bata gari suka lalata manyan wayoyin rarraba wutar lantarki a Gwagwalada-Kukwaba-Apo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

A ranar Litinin ne cibiyar samar da wutan lantarkin Najeriya ta sake durkushewa, lamarin da ya jefa kasar cikin duhu.

Da misalin karfe 1 na rana ne aka rahoton durkushewar cibiyar, kamar yadda Ndidi Mbah, manajan hulda da jama'a na hukumar rarraba wutar lantarkin Najeriya (TCN) ya sanar.

Kara karanta wannan

Ayi hattara: Babbar gadar fita daga Legas ta ruguje, ta haddasa cunkoso

Cibiyar samar da lantarki a Najeriya ta durkushe
A ranar litinin ne cibiyar samar da wutan lantarkin Najeriya ta sake durkushewa, lamarin da ya jefa kasar cikin duhu. Hoto: TCN
Asali: Getty Images

A cewar Mr Mbah:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Lamarin ya faru misalin karfe 1:49 na rana. Amma zuwa yanzu an gyara,"

Wannan shi ne karo na uku da irin hakan ta faru a cikin shekarar 2023, inda a baya hakan ta taba faruwa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

An lalata manyan wayoyin rarraba wutar lantarki a Gwagwalada

Radio Nigeria ta ruwaito yadda a ranar 14 ga watan Satumba da 19 ga watan cibiyar ta durkushe, amma aka gyara matsalar a lokacin.

A wani labarin kuma, a safiyar Talata Mbah ya ce an lalata manyan wayoyin rarraba wutar lantarki mai karfin 132(KV) daga kamfanin ta da ke Gwagwalada-Kukwaba-Apo.

Mbah ya kara da cewa wannan ta'addancin ya faru ne da misalin karfe daya na daren ranar 10 ga watan Disamba, 2023.

Ya ce kamfanin na iya bakin kokarinsa wajen ganin ya gyara inda aka lalata.

Kara karanta wannan

Kasafin Tinubu ya fusata Arewa, ba a ware sisi domin aikin wutan Mambilla a 2024 ba

Ministan Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya albishir kan wutar lantarki

A ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa, ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya ce kudurin dokar wutar lantarki na 2023 zai inganta samar da wutar a Najeriya.

A cewar ministan, idan har aka kaddamar da kudirin dokar, to Najeriya na iya samun tsayayyar wutar lantarki birni da kauyuka, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel