Ana Cikin Barazana a Zamfara, ‘Yan Bindiga Sun Kona Kayan Abinci Duk da Kashe Mutane

Ana Cikin Barazana a Zamfara, ‘Yan Bindiga Sun Kona Kayan Abinci Duk da Kashe Mutane

  • ‘Yan bindiga sun sake shiga Zamfara a karshen makon jiya, wannan karo har da kona abincin da aka boye
  • Da ‘yan bindiga su ka kai hari garin Gidan Shaho, sun rika bi gidajen da aka tara kayan abinci, suna konawa
  • Miyagun ‘yan bindigan sun kashe mutane a Nasarawar Zurmi kuma sun sace dukiyar mutane cikin dare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Zamfara - Akalla Bayin Allah uku ne aka tabbatar da cewa sun mutu a wani hari da ‘yan bindiga su ka kai a garuruwan jihar Zamfara.

A ranakun Juma’a da Asabar, Premium Times ta samu labari an kashe mutane tare da sace wasu a Gidan Shaho da Nasarawar Zurmi.

Gwamna Dauda Lawal
Gwamnan Zamfara tare da Sojoji Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Wannan labari mara dadi ya auku ne a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara da aka yi shekaru ana fama da matsalar ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Assha: Yan bindiga sun halaka mutum 4 a Plateau, sun kona gidan basarake

Zamfara: Hari a ranar Juma'a

A ranar Juma’a aka shiga kauyen Gidan Shaho da kimanin karfe 10:00 na dare, aa shafe akalla awa biyu ana ta’adi aka harbi wani mutum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani matashi ya ce ‘yan bindigan sun kuma harbi wasu mutane biyu wanda yanzu haka su na kwance a babban asibitin da ke garin Zurmi.

Rahoton ya ce ana zargin ‘yan ta’addan sun shiryawa harin da kyau domin sun rika zaben gidajen da za su shiga ganin sun rika kona abinci.

An kona rumbunan abinci a Zamfara

“Sun tsara harin da kyau domin (‘yan bindigan sun rika zaben gidajen da za su kai hari. A mafi yawan gidajen da su ka shiga, sun kona rumbunan abinci.
Mun yi imani cewa sun samu labarin wadanda su ke da kayan abinci."

- Inji wani matashi a Zurmi

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun kuma ta’adi a Abuja, an yi garkuwa da mace da yaranta har da jariri

Jama'an Zamfara sun fara barin Zurmi

Da aka auka Nasarawara Zurmi a ranar Asabar, an kashe wasu maza biyu, sannan an yi garkuwa da mutane har hudu da ke zaune a kauyen.

Ba a samu labarin an harbe wani ba, amma an saci kaya gidajen da aka shiga. A halin yanzu mutane su na ta tserewa daga garin Zurmi.

Rikicin siyasar APC da PDP a Zamfara

A gefe guda kuwa 'yan APC da PDP su na ta rikici har an ji Bello Muhammad Matawalle ya kira Dauda Lawal makaryaci da mayaudari.

A wani sabon martani da tsohon gwamna Bello Matawalle yayi wa magajinsa, ya fadi yadda Dauda ya nemi ya hada Zamfara da bashin N30bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng