Zamfara na fama da 'yan gudun hijira 700,000 gidaje 3,000 sun halaka, Matawalle
- Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce akwai 'yan gudun hijira 700,000 daga jihar Zamfara
- Duk da rasa gidaje 3,000 da aka yi a jihar, gwamnan ya sha alwashin samar da lafiya tare da walwala ga 'yan gudun hijiran
- Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Kabiru Balarabe, ya ce jihar ba za ta sassauta ba, za ta cigaba da matsawa 'yan bindiga lamba
Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Bello matawalle, ya ce akwai sama da mutane dubu dari bakwai da suka rasa gidajensu kuma su ke rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira a jiharsa.
Gwamnan ya sanar da Daily Trust cewa, gwamnatin jihar na fafutukar samar wa jama'ar magani da walwala, wadanda suka bar gidajensu sakamakon addabarsu da 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane suka yi.
A ranar Alhamis, gwamnatin ta karba mutum 185 ta hannun 'yan sanda wadanda aka karbo daga masu garkuwa da mutane.
Idan za a tuna, mahaifin kakakin majalisar jihar Zamfara, Alhaji Mu'azu Magarya, wanda aka sace a watan Augusta, ya rasu a hannun 'yan bindigan bayan kwashe makonni a hannunsu.
An yi jana'izar mamacin duk da har yanzu ba a samu gawarsa daga hannun 'yan ta'addan ba, Daily Trust ta ruwaito.
An gano cewa, wadanda aka sace a sassa daban-daban na jihar an bar su babu abinci, hakan yasa suka mayar da hankali su na cin ciyawa domin su rayu.
Daya daga cikin wadanda aka samu din mai suna Iklima Murtala, ta ta yi ikirarin cewa mutum 17 ne suka rasu sakamakon rashin abinci.
A yayin karbar wadanda aka ceto a madadin gwamnatin jihar, sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Kabiru Balarabe ya ce, "Gwamnatin jihar za ta cigaba da matsa wa 'yan bindigan lamba har sai sun saduda."
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ayuba Elkana, ya ce matsanta lamba da rashin abinci ya sa 'yan bindigan ba su iya barnar da suka saba yi.
Kaduna: 'Yan sanda sun ceto mutum 6 da aka yi garkuwa da su
A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta ce jami'an ta sun ceto mutum shida da aka sace a kan babbar hanyar Barde zuwa Keffi da ke karamar hukumar Kafanchan ta jihar.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Mohammed Jalige, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar ranar Alhamis a garin Kaduna.
Jalige ya ce a ranar 5 ga watan Oktoba, jami'an 'yan sanda sun samu rahoton garkuwa da mutane da aka yi ranar hudu ga wata wurin karfe shida da rabi kan titin Barde zuwa Keffi, "cike da hankali tare da salo aka bibiye su tare da kai wa ga 'yan fashin dajin".
Asali: Legit.ng