Likafa Ta Ci Gaba: Bidiyon Kwandastan Mota Dauke Da POS Ya Bar Mutane Baki Bude

Likafa Ta Ci Gaba: Bidiyon Kwandastan Mota Dauke Da POS Ya Bar Mutane Baki Bude

  • An gano wani kwandastan mota dauke da na'urar POS yayin da yake kiran fasinjoji da su shiga motarsa a Lagas
  • A wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, an gano kwandastan yana kiran suna unguwannin da zai je sannan cewa yana da POS
  • Jama'a sun yi martani inda wasu ke kallon hakan a matsayin wata hanya ta damfarar mutane guminsu

Lagas - Yayin da ake ci gaba da fama da karancin naira a tsakanin yan Najeriya, an gano wani kwandasta a jihar Lagas yana kiran fasinjoji tare da fada masu cewa yana da POS.

A cikin bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya, an gano kwadastan motar rike da na'urar POS rike a hannunsa.

Kwadastan mota
Likafa Ta Ci Gaba: Bidiyon Kwandastan Mota Dauke Da POS Ya Bar Mutane Baki Bude Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar Punch ta wallafa a shafinta na Twitter, an saki bidiyon kwandastan ne a ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu, an kuma jiyo shi yana cewa: "Ketu, Ojota, Mile12, POS."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Yan Daba Sun Tafi Gidan Wani Dan Gani Kashe Nin Tinubu, Sun Lakada Wa Mahaifiyarsa Duka, Sun Kona Motarsa

Wannan al'amari ya bai wa mutane mamaki inda wasu suka ce lallai akwai hikima tattare da wannan sabon salon. Wasu sun ce yanzu babu ruwansu da biyan yan gareji kudi mara dalili.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma wani ya ankarar da mutane da su lura kada a yi wa akawun dinsu tatas.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Reuben Matthew ya ce:

"A kalla ba sai sun dunga biyan wadannan yan garejin marasa amfani ko sisin kwabo ba. Hakan ya yi kyau."

@ife_cyntia ta ce:

"Kwandastan bai son jin wai manufar sabon kudi ya hana ka fita."

Lekan Bambo:

"Hakan ya fi kuma wannan tunani ne mai kyau."

Osteve ya ce:

"Ina son gja. Na so ace shugabannin siyasarmu na gani sama da ramin hancinsu."

Sharon Olofintuyi ta ce:

"Ku jira har sai sun fara yashe asusun mutane."

Kara karanta wannan

'Cashless': Maroki ya waye, ya buga kalangu a wani bidiyo, ya ba lambar akanta

Wata mazauniyar jihar Legas mai suna Hajara Abdullahi ta ce lallai wannan ci gaban zai taimaka sosai domin suna matukar shan wahala kafin su samu kudi da za su gudanar da harkokinsu.

Ta ce:

"Gaskiya ya kamata sauran kwandastoci su yi koyi da wannan mai mota domin dai ana shan wahala sosai musamman mu mazauna jihar Legas.
"Rannan haka na taka tun daga isale Oja Agege har zuwa Iyana Ipaja toh dole ne fitan gashi babu tsabar hawa mota. Amma kunga idan sauran masu mota suka fara yawo da POS sai mu samu saukin abun."

Matashi ya fasa asusun katako da ya shafe shekaru biyu yana tara kudi a cikinsa

A wani labarin, mun ji cewa wani matashi ya baiwa mutane da dama mamaki bayan ya fasa asusun ajiyarsa na katako wanda ya shafe tsawon shekaru biyu yana zuba kudi a ciki.

Kamar yadda matashin ya bayyana, niyansa shine sai bayan shekaru hudu zuwa biyar zai fasa idan ba son sauya kudi da CBN ya yi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel