Labari Mai Dadi Yayin da Gwamnatin Tinubu Ta Fara Rabawa Talakawa N20,000 a Jihar Arewa

Labari Mai Dadi Yayin da Gwamnatin Tinubu Ta Fara Rabawa Talakawa N20,000 a Jihar Arewa

  • Shugaban kasa Bola Tinubu bai dauki shirinsa na sabonta fata a kasar da wasa ba
  • Shugaban kasar ya kafa wata ma'aikata a jihar Kogi domin kawar da talauci a kasar da tallafawa mutane da kudi
  • Betta Edu ta tabbatar da ci gaban yayin da ta kaddamar da shirin tallafi na N20,000 a jihar Kogi, domin rage radadin cire tallafin mai a tsakanin talakawa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta mayar da hankali sosai wajen cimma ajandarta na sabonta fata.

Hakan ya kasance ne yayin da Ma'aikatar jin kai da kawar da talauci karkashin jagorancin Dr Betta Edu, ta kaddamar da shirin rabawa marasa karfi N20,000 a jihar Kogi, a ranar Talata, 5 ga watan Disamba, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Manyan Arewa: Take-taken Tinubu sun nuna bai damu da gyara tsaron Arewa ba

Tinubu ya fara rabawa talakawa N20,000 a jihar Kogi
Labari Mai Dadi Yayin da Gwamnatin Tinubu Ta Fara Rabawa Talakawa N20,000 a Jihar Arewa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Dr Betta Edu Media Watch
Asali: Facebook

Yayin da take kaddamar da shirin, Dr. Edu, ta yi bayanin cewa tallafin da aka bai wa marasa karfin ba bashi bane kuma ba za su biya ba, rahoton Nigerian Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Edu ta ce Shugaban kasa Tinubu ya jajirce don ganin ya fitar da akalla yan Najeriya miliyan 50 daga kangin talauci.

Ta kara da cewar:

"Don cimma wannan, shugaban kasar ya kafa wata tawaga don ta gano talakawa a cikin mutanenmu sannan ta zo da jerin shirye-shirye da zai taimakawa tattalin arzikin talaka."

Kalli bidiyo yayin da Betta Edu ta ziyarci al'ummar Kabbawa a jihar Kogi

Gwamnatin Tinubu za ta ba yan Najeriya bashi

A wani labarin, mun ji cewa domin tallafawa kanana da matsakaitan 'yan kasuwa, gwamnatin Tinubu ta kaddamar da shirin "Renewed Hope Micro, Small and Medium Enterprise (MSME)".

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya tsokano Rigima da ikirarin babu aikin da Buhari ya yi a shekara 8

An kaddamar da shirin MSME don fadada shirin "Market-Moni", da nufin tallafawa talakawa miliyan 1.5 da jarin naira dubu 50 kowanne mutum daya.

A baya, an fi sanin shirin da suna "shirin tallafawa talakawa 'yan kasuwa na gwamnati (GEEP)", kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa uwar gidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu ce ta kaddamar da shirin a Abuja, inda ta raba takardun ceki ga wadanda za su ci gajiyar shirin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel