Abba Gida-Gida Ya Kirkiri Asibitin Tafi da Gidanka Don Amfanin kanawa,Ya Tura Sakon Gargadi

Abba Gida-Gida Ya Kirkiri Asibitin Tafi da Gidanka Don Amfanin kanawa,Ya Tura Sakon Gargadi

  • Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir ya kaddamar da asibitin tafi da gidanka don kare rayuka da kuma ba da kulawan gaggawa
  • Gwamnan ya samar da bas bas da zasu ke yawo a Kano don taimakawa marasa lafiya a kokarimsa na inganta bangaren lafiya
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan a bangaren yada labarai, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya kaddamar da asibitin tafi da gidanka wanda zai taimaka wurin kulawar gaggawa.

An ware bas bas da za su taimaka wurin kulawar gaggawa da ke dauke da komai a ciki wanda za su ke yawo a Kano.

Kara karanta wannan

Bani da katabus: Wanda ya kone takardar digirinsa ya yi bayanin dalilansa na bankawa takardunsa wuta

Abba Kabir ya samar da asibitin tafi da gidanka a jihar Kano
Abba Gida-Gida ya kaddamar da bas bas don samar da kulawar gaggawa a harkar lafiya. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Twitter

Wane shiri Abba Kabir ya yi a harkar lafiya?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan a bangaren yada labarai, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bature ya ce Gwamna Abba Kabir ya himmatu wurin tabbatar da cewa ya bai wa harkar lafiya kulawa na musamman, cewar Daily Trust.

Babban sakataren hukumar asibitoci a jihar, Dakta Mansur Mudi ya gargadi direbobim bas din da ma'aikatan lafiya kan amfani da su ta wata hanya.

Wane gargadi Abba Kabir ya yi?

Mudi ya sha alwashin daukar mummunan mataki kan wadanda aka samu da aikata laifin amfani da su ta wata hanya.

Ya ce:

"An samar da bas bas din ne don marasa lafiya kadai, duk wanda aka samu da laifin karkatar da su ta wata hanya zai fuskanci fushin hukuma."

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama hadimin Abba Gida-Gida da wani kan laifi 1 tak

Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin jihar ta ce ta bai wa bangaren lafiya da ilimi fifiko don inganta tattalin arzikin jihar, Daily Nigerian ta tattaro.

Abba Kabir ya kaddamar da biyan fansho

A wani labarin, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da biyan kudaden fansho har naira biliyan shida a jihar.

Gwamnan ya ware kudaden ne don rage yawan basukan 'yan fansho da kuma giratuti a jihar.

Akalla ma'aikata dubu biyar ne za su ci gajiyar inda gwamnan ya ce gwamnatin baya ta bar musu bashi har biliyan 48.

Asali: Legit.ng

Online view pixel