Da Gaske an Ware Biliyan 21 Don Gyaran Gidan Shugaban Ma'a'ikatan Tinubu? Gaskiya Ta Yi Halinta

Da Gaske an Ware Biliyan 21 Don Gyaran Gidan Shugaban Ma'a'ikatan Tinubu? Gaskiya Ta Yi Halinta

  • Yayin da ake ta cece-kuce kan kudaden kasafin Tinubu, Femi Gbajabiamila ya yi martani a kai
  • Shugaban ma'aikatan ya bayyana cewa karya aka shirya masa kan wai an ware biliyan 21 don gyaran gidansa a Abuja
  • Femi ya yi wannan martani ne a yau Laraba 6 ga watan Disamba a shafinsa na X inda ya ce a gidan na musamman ya ke zaune

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban ma'akatan Gwamnatin Tarayya, Femi Gbajabiamila ya yi martani kan jita-jitar da ke yadawa na kasafin kudi a ofishinsa.

Femi na magana kan cewa an ware wa ofishinsa makudan kudade har naira biliyan 21 a kasafin da Shugaba Tinubu ya mika gaban Majalisa.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Dattawan Arewa sun fadi abin da ya kamata manyan sojoji su yi, sun fadi dalilansu

Femi Gbajabiamila ya yi martani kan ware biliyan 21 don gyaran gidansa da ke Abuja
Femi Gbajabiamila ya karyata ware biliyan 21 don gyaran gidansa a Abuja. Hoto: Femi Gbajabiamila.
Asali: Twitter

Mene ya jawo kace-nace kan kasafin kudin da Tinubu ya mika?

Gbajabiamila ya ce wannan magana ba ta da tushe inda ya ce kudaden da ake magana an ware su ne don gyaran gidan shugaban kasa a Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon kakakin Majalisar ya yi martanin ne a shafinsa na X a yau Laraba 6 ga watan Disamba.

Wane martani Femi ya yi kan kasafin kudin?

Femi ya yi martani da cewa:

"Naga rahoton da ake yada wa a kafofin sadarwa kan kasafin kudin 2024 musamman a ofishin shugaban ma'aikata.
"Ganin kuskuren da ke cikin rahoton ya zama wajibi na yi martani a kai, babu inda aka ware kudade don gyaran gida na, ina zaune ne a gidan mai zaman kansa a Abuja.
"Kudaden an ware su ne don gyaran gidan shugaban kasa da mataimakinsa da ke Barikin Dodan a Legas."

Kara karanta wannan

Manyan Arewa: Take-taken Tinubu sun nuna bai damu da gyara tsaron Arewa ba

Femi ya ce kudaden da ake magana a kai an bayyana su a cikin kasafin kudin wanda ya bambanta da yadda ake yadawa a kafofin sadarwa, cewar Arise TV.

Tinubu ya fara biyan albashin watan Nuwamb

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya fara biyan albashin watan Nuwamba na ma'aikatan da su ke da matsalar IPPIS.

Wannan na zuwa ne yayin ma'aikata da dama albashinsu ya makale musamman na watan Nuwamba saboda matsaloli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel