Abdullahi Ganduje Shugaban APC Ya Yi Ganawari Sirri Da Oshiomhole

Abdullahi Ganduje Shugaban APC Ya Yi Ganawari Sirri Da Oshiomhole

  • Kwamared Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa ya yi ganawar sirri da Abdullahi Ganduje, shugaban APC mai ci
  • Sanatan na Edo ta Arewa ya isa harabar sakatariyar jam'iyyar ta APC ne misalin karfe 4.15 na yammacin Talata kuma ya samu tarba mai kyau
  • Bayan gaisuwa da Ganduje, mutanen biyu sun shiga daga ciki suka yi taron sirri na kimanin mintuna 35 sannan Oshiomhole ya fito ya shiga mota ya yi gaba

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole, a ranar Talata, ya kai ziyarar bazata hedkwatar jam'iyyar All Progressives Congress, APC, da ke Abuja.

Sanatan mai wakiltar Edo ta Arewa, wanda ya isa sakatariyar jam'iyyar misalin karfe 4.15 na yamma, ya samu babban tarba daga shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

"Akwai Haske": Abdulsalami Ya Yi Magana Kan Tattaunawarsu Da Sojojin Juyin Mulkin Nijar

Hakan na zuwa ne kwana daya bayan rantsar da ministoci 45 na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Oshiomhole bai yi magana da menama labarai ba

Bayan gaisawa, mutanen biyu sun yi taron sirri na misalin mintuna 35 kafin Oshiomhole, wanda tsohon shugaban APC na kasa na ya fito ya shiga motarsa ba tare da yin magana da yan jarida ba.

Dakaci karin bayani ...

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Asali: Legit.ng

Online view pixel