Gwamnatin Najeriya ta fara gudanar da gyare gyare a matatun mai guda 3

Gwamnatin Najeriya ta fara gudanar da gyare gyare a matatun mai guda 3

Hukumar man fetir Najeriya, NNPC, ta kaddamar da fara gudanar da gyaran matatun man fetir na Najeriya, inda ta fara da babbar matatar mai dake garin Fatakwal na jahar Ribas, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban NNPC, Mele Kyari ne ya bayyana haka yayin wani taron masana a harkar man fetir daya gudana a jahar Legas a ranar Alhamis, 22 ga watan Agusta, inda yace suna sa ran zuwa shekarar 2023 zasu kammala gyaran matatun mai gaba daya.

KU KARANTA: Madalla: Sojojin Najeriya sun bankado wani mugun shiri da Boko Haram ta yi a Borno

Kyari ya koka game da yadda Najeriya ta kasance kasa mai dimbin arzikin man fetir, amma kuma ta buge da sayo mai daga kasashen waje, sai dai ya danganta hakan ga lalacewar matatun man fetir Najeriya da yasa basa iya samar da mai.

“Don haka muna bukatar karin zuba jari don ciyar da harkar man fetir gaba a Najeriya, da wannan ne yasa zan yi iya bakin kokarina a matsayi na shugaban NNPC don ganin na tayar da komadan matatun man Najeriya na Warri, Fatakwal da Kaduna domin su samar da litan mai 445,000 a duk rana.

“Haka zalika muna aiki tare da kamfanoni masu zaman kansu dake kokarin samar da kananan matatun mai a Najeriya, bugu da kari zamu bayar da dukkanin gudunmuwa ga kamfanin Dangote dake gina katafaren matatar mai da zata samar da lita 650,000 na tataccen mai a duk rana.

“Burina shi ne naga Najeriya tana fitar da tataccen man fetir zuwa shekarar 2023.” Inji shi.

Daga karshe shugaban NNPC ya yi kira gwamnati da ta samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari, wanda hakan zai rage makudan kudaden da gwamnati take kashewa a fannin, sa’annan ya nemi majalisar dokokin Najeriya ta kammala aiki a kan dokar masana’antar man fetir PIGB, don ta fara aiki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng