Abin Farin Ciki: Baturiya Ta Sauke Al-Kur’ani Tana da Shekaru 62 a Jihar Kano
- Wata baturiya mai shekaru sittin da biyu ta samu nasarar yin saukar Al-Kur'ani a wata makarantar islamiyya a Kano
- Baturiyar 'yar asalin kasar Burgariya ta ce ta samu nutsuwa da farin ciki a addinin Musulunci
- Shekaru talatin kenan Liliana na rayuwa a jihar Kano tun bayan auren wani bahaushen dan kasuwa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kano - Dattijuwa mai shekaru sittin da biyu, Liliana Mohammed, daga kasar Bulgariya ta yi saukar Al-Kur'ani a jihar Kano.
Shekaru talatin ke nan Mrs Mohammed ke zaune a Kano tun bayan auren wani bahaushen dan kasuwa, marigayi Ibrahim Sambo a Bulgariya.
Yadda baturiya ta fara koyon Al-Kur'ani
Shekaru kusan ashirin mahaifiyar yara biyun ta yi riko da addini ka'in da na'in, inda ta fara koyon yadda ake karanta Al-Kur'ani don samun shiriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na fara koyon karatun Al'Kur'ani a gida, inda wata malama Hafsa ke zuwa tana koya min. Mun fara tun daga farfaru da babbaku, har na koyi haruffan larabci.
"Daga nan ne kuma na fara koyon hada baki, da karanta ayoyi, surori, har dai zuwa wannan rana da na yi sauka a makarantar Islamiyya."
A cewar Liliana.
Na samu nutsuwa a addinin Musulunci - Mrs Mohammed
Mrs Mohammed dai ta yi saukar ne tare da wasu dalibai uku a makarantar Islamiyya ta Mamba'irrahman da ke Kano ranar Asabar, rahoton Daily Nigerian.
Ta ce:
"Na samu nutsuwa da farin ciki a cikin addinin Musulunci. Al'Kur'ani ya zamar min haske da shiriya. Idan ina karanta ayoyin Allah, ina samun kwanciyar hankali"
"Duk da cewa tsufa ya riske ni, amma hakan bai hana ni fara haddace Al-Kur'ani ba, yanzu haka na fara."
Da ta ke jawabi kan rayuwa a Kano, Liliana ta ce garin ya yi mata kasancewar Musulmai sune suka fi yawa, kuma akwai kwanciyar hankali da hanyar ilimi.
A cewar ta, lokutan sallah da azumi a jihar Kano ya fi yi mata dai dai sabanin na wasu kasashen duniyar.
Rikakken dan daba a Kano, Hantar Daba, ya mika wuya
A wani labarin, mahaifiyar rikakken dan daba a jihar Kano, ta yi ta-maza inda ta mika shi ga 'yan sandan jihar, Legit Hausa ta ruwaito.
A baya ne rundunar 'yan sanda ta sanya kyautar naira dubu dari biyar ga duk wanda ya gano inda dan dabar mai suna Hantar Daba ya ke.
Asali: Legit.ng