Shugaba Tinubu Ya Dawo Najeriya Ana Tsaka da Jimamin Kisan Mutane a Kaduna

Shugaba Tinubu Ya Dawo Najeriya Ana Tsaka da Jimamin Kisan Mutane a Kaduna

  • Bola Ahmed Tinubu ya isa Abuja, babban birnin tarayya bayan halartar taron sauyin yanayi na majalisar ɗinkin duniya a Dubai
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ta kiraye-kiraye ya ɗauki mataki kan kisan masu Maulidi a jihar Kaduna
  • Yayin zamansa a Dubai, Shugaba Tinubu ya gana da shugabannin ƙasashe da dama da Sarkin Ingila

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo babban birnin tarayya Abuja bayan halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi karo na 28.

Taron dai ya gudana ne a birnin Dubai da ke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), kamar yadda Channels tv ta tattaro.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Dawo Najeriya Ana Tsaka da Jimamin Kisan Mutane a Kaduna Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ayyukan da Tinubu ya yi a Dubai

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya yi magana kan kisan Musulmai a Kaduna

Baya ga taron da shugaban ƙasa ya halarta a Dubai, Tinubu ya kuma samu damar ƙeɓewa da wasu shugabannin kasashen duniya sun tattauna kan wasu batutuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan tafiya, Bola Tinubu ya gana da Sarki Charles na ƙasar Ingila, shugaban ƙasar UAE da shugabannin wasu kasashe da abokan hulda na bangarori daban-daban don cimma matsaya.

Shugaba Tinubu ya kuma shaida rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta gaggawa tsakanin Najeriya da Jamus domin inganta samar da wutar lantarki a Najeriya.

Bayan haka, shugaban kasar ya karɓi bakuncin wani babban taro na masu ruwa da tsaki da masu zuba jari kan Kasuwar Carbon ta Najeriya da shirin kaddamar da motocin bas na lantarki.

Shugaban ya yi waɗannan taruka da sa hannu kan yarjejeniyar ne a gefe ɗaya baya ga taron sauyin yanayi karo na 28 da ya kai shi birnin Dubai.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun halaka direba tare da yin awon gaba da fasinjoji a wani sabon hari

A ranar 29 ga Nuwamba, 2023, Tinubu ya bar Abuja zuwa Dubai domin halartar taron da ake sa ran kammalawa a ranar 12 ga Disamba, 2023 cewar Daily Trust.

A halin yanzu, Shugaban ya dawo a kan gaba yayin da ake tsaka da jimamin kuskuren sojoji na jefa bam kan Musulmai masu Maulidi a kauyen Tudun Biri, Kaduna.

Wannan hari dai ya yi ajalin mutane sama da 100 kawo yanzu, kuma wasu da dama na jinya a asibitin Barau Dikko.

Gwamnatin tarayya zata biya diyya

A wani rahoton kuma Muhammad Badaru, Ministan tsaro ya ce gwamnatin tarayya za ta biya diyya ga dangogin wadanda bam ya kashe a Kaduna.

Kwanan nan sojojin sama su ka yi kuskuren kashe wasu masu maulidi a kauyen Tudun Birni da ke karamar hukumar Igabi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262