Yanzu: Kotu Ta Yanke Hukunci Mai Tsauri Kan Masu Daukar Nauyin Boko Haram 4, Karin Bayani

Yanzu: Kotu Ta Yanke Hukunci Mai Tsauri Kan Masu Daukar Nauyin Boko Haram 4, Karin Bayani

  • Mai shari'a Binta Nyako da Mai shari'a Emeka Nwite, sun yankewa masu daukar nauyin Boko Haram hudu hukunci tare da tura su magarkama
  • Alkalan sun yanke hukuncin ne a babbar kotun tarayya da ke zama a Dawaki, Abuja, a ranar Litinin, 4 ga watan Disamba
  • Gwamnatin tarayya ta samu hukunta wasu mutane hudu da ke daukar nauyin yan ta’adda bayan ta gurfanar da su a gaban shari’a ta musamman

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Dawaki, Abuja ta hukunta tare da daure masu daukar nauyin Boko Haram hudu.

Mai shari'a Binta Nyako da Mai shari'a Emeka Nwite sun tura yan ta'addan - Modu Aisami, Zana Zarama, Umar Mohammed da Bunu Kame magarkama - bayan sun amsa tuhume-tuhumen da ake yi masu, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Akwai kotun Allah": Martanin jama'a bayan kotu ta yanke hukunci a shari'ar Abba da Ado Doguwa

Kotu ta hukunta masu daukar nauyin Boko Haram
Yanzu: Kotu Ta Aika Masu Daukar Nauyin Boko Haram 4 Magarkama, Karin Bayani Hoto: Appeal Court
Asali: UGC

Mai taimakawa Atoni Janar na tarayya na musamman kan harkokin sadarwa da wayar da kai, Kamarudeen Ogundele, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a daren ranar Litinin, 4 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ogundele ya ce wadanda ake karan, wadanda aka gurfanar da su daban-daban sun amsa tuhume-tuhumen da ake masu sannan suka roki kotu ta yi masu sassauci, rahoton The Punch.

A bisa karar da Daraktan shigar da kara na kasa (DPPF) Mista M. B. Abubakar ya shigar, daya daga cikin wadanda ake tuhumar, Aisami, ya bayar da kudade ga kungiyar ta’addanci ta hanyar siyan kayan abinci daga hannunsu.

An zarge shi da sanin cewa za a yi amfani da kudaden da aka samu daga hada-hadar wajen aikata ta'addanci.

Mai shari’a Nyako ta hukunta Aisami ne a kan tuhume-tuhume na 2 da 3.

Kara karanta wannan

Dubun wasu hatsabiban 'yan bindiga 8 da suka addabi mutane ya cika a jihar Kaduna

“Na same shi da laifi kamar yadda ake tuhumar sa kuma an yanke masa hukunci daidai da haka.
“Saboda haka na yanke hukuncin daurin shekaru 20 ga wanda aka samu da laifi kan kowane laifi. Za su gudana a lokaci guda."

Mai shari'ar ta kuma yanke hukuncin daurin shekaru 10 ga wanda ake kara na biyu, Zarama, bisa samunsa da laifin boye sunan wani dan Boko Haram, Modu Sulum.

Mai shari’a Nyako ta ce hukuncin daurin zai ci gaba daga ranar da aka kama masu laifin tare da tsare su a magarkama.

Yayin da mai shari’a Nwite, a hukuncinsa ya yanke daurin shekaru 10 a gidan yari ga sauran biyun Mohammed da Kame.

Za a hukunta masu daukar nauyin Boko Haram

A baya Legit Hausa ta kawo cewa babban alkalin babbar kotun tarayya, Mai shari’a John Tsoho, ya fitar da wata sabuwar alkibla a batu shari’ar ta’addanci da ke gabanta.

A halin yanzu dai shari’ar shugaban 'yan awaren Biafra, Nnamdi Kanu, da 'yan canjin da ake tuhumarsu da laifin daukar nauyin ayyukan ta’addanci suna gaban kotun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng