Kotu Ta Yi Hukunci Kan Shari’ar Mai Taimakon Boko Haram da Kudade da Kuma DSS, Ta Fadi Dalili

Kotu Ta Yi Hukunci Kan Shari’ar Mai Taimakon Boko Haram da Kudade da Kuma DSS, Ta Fadi Dalili

  • Yayin da ake ci gaba da shari’ar dan Boko Haram da hukumar DSS, babbar kotun Tarayya ta yi hukunci kan shari’ar
  • Ana zargin Abba Maina da taimakawa kungiyar Boko Haram da kudade don gudanar da ayyukansu na ta’addanci
  • Abba ya shigar da hukumar DSS a kotu kan kame shi ba tare da wasu hujjoji ba na tuhumar da su ke masa

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babbar kotun Tarayya ta kori karar wanda ake zargi da bai wa Boko Haram kudade kan hukumar DSS.

Wanda ake zargin, Abba Maina ya maka hukumar DSS ne a kotu kan zargin tuhumarsa babu dalili kan zargin bai wa kungiyar kudade.

Kara karanta wannan

Kotu ta fadi ranar hukuncin shari'ar dan China kan zargin kisan budurwarsa Ummita

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar dan Boko Haram da hukumar DSS
Kotu ta raba gardama kan shari'ar dan Boko Haram da hukumar DSS. Hoto: DSS.
Asali: Twitter

Wane hukunci kotun ta yanke?

Mai Shari’a, Inyang Ekwo a jiya Talata 28 ga watan Nuwamba ya yi watsi da karar saboda kasancewar irin karar a gaban kotun Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan Satumbar 2022, hukumar DSS ta kama Maina a wani banki a birnin Abuja da zargin taimaka wa kungiyar da kudade.

Hukumar ta ce ta kama Maina ne yayin da ya je banki don bincikar dalilin rufe masa asusun bankinsa.

Mene DSS ke zargin Maina a kai?

TheCable ta tattaro cewa DSS ta samu bayanan sirri cewa an shirya bai wa wani mai samar da makamai ga kungiyar makudan kudade don yin wani aiki.

Hukumar ta ce ana zargin wani mai suna Kaura da bashi miliyan 10 don debo mayakan Boko Haram daga Borno zuwa Kaduna.

Yayin tura kudaden, Kaura ya bukaci asusun bankunan wasu mayakan Boko Haram, Baba Guraba da Bayero da ke karamar hukumar Bama, cewar PM News.

Kara karanta wannan

Yanzu: Kotun Daukaka Kara ta kori kakakin majalisar Bauchi

Yayin hukuncin, Ekwo ya ce ya kori karar ce saboda saba dokokin kotu ganin cewa akwai irin karar a kotun Abuja.

Daga bisani, Alkalin kotun ya yi fatali da karar saboda saba ka’idar kotuna da aka yi yayin shigar da hukuncin.

DSS ta gurfanar da dan Boko Haram a kotu

A wani labarin, Hukumar DSS ta sake gurfanar da wani da ake zargi da kai harin bam kan masallacin Kano.

Ana zargin Hussaini Ismail da kisa a harin kan babban masallacin a shekarar 2014 da ya yi ajalin mutane da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel