Da dumi-dumi: Kotu za ta yi shari'ar sirri ga masu daukar nauyin Boko Haram da Nnamdi Kanu

Da dumi-dumi: Kotu za ta yi shari'ar sirri ga masu daukar nauyin Boko Haram da Nnamdi Kanu

  • Yanzu haka dai an hana ‘yan jarida daukar rahotanni kan shari’ar ta’addanci da ke gaban babbar kotun tarayya
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da babban alkalin kotun, Mai shari’a John Tsoho ya sanar da sabon tsarin gudanar da shari’ar ta’addanci
  • Irin wadannan laifuka sun hada da na shugaban 'yan awaren Biafra Kanu, masu daukar nauyin Boko Haram, da dai sauransu

Babban alkalin babbar kotun tarayya, Mai shari’a John Tsoho, ya fitar da wata sabuwar alkibla a batu shari’ar ta’addanci da ke gabanta, Daily Trust ta rahoto.

A halin yanzu dai shari’ar shugaban 'yan awaren Biafra, Nnamdi Kanu, da 'yan canjin da ake tuhumarsu da laifin daukar nauyin ayyukan ta’addanci suna gaban kotun.

Mai shari’a Tsoho ya ce sabuwar alkiblar shari'ar ita ce ta yin amfani da ikonsa na tsarin mulki kamar yadda yake a sashe na 254 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 (kamar yadda aka gyara).

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Kwankwaso ya koma NNPP, ta yiwu Tinubu kuma ya koma SDP, inji majiya

Da dumi-dumi: Kotu za ta yi shari'ar sirri ga masu daukar nauyin Boko Haram da Nnamdi Kanu
Da dumi-dumi: Kotu za ta yi shari'ar sirri ga masu daukar nauyin Boko Haram da Nnamdi Kanu | Hoto: vamguardngr.com
Asali: UGC

A karkashin sabon tsarin, kotun ta ce an haramta yada labarai game da shari'ar a kafafen yada labarai har sai kotun ta ba da umarnin haka.

Sai dai, a bangare guda, tsarin ya bayyana cewa, a wani yanayin alkali zai iya yarda kafafen yada labarai su dauki shari'o'in, kamar yadda TVC News ta tattaro.

A cewar sanarwar da kotun ta fitar:

“Mutumin da ya saba wa umarni ko ka'idar da aka bayar a karkashin wadannan ka’idojin, za a tuhumi shi da aikata wani laifi da ya saba wa sashi na 34 (5) na dokar ta’addanci (Kariya) ta 2011 (kamar yadda aka gyara)."

Ya ci gaba da cewa:

“Alkalai kawai; sauran muhimman ma’aikatan kotuna da jami’an tsaro da ke da hannu a cikin lamarin da motocinsu NE za su samu damar shiga harabar kotun.”

Kara karanta wannan

Ganin saukar bakon jirgin sama: Jami'an tsaro sun bincike dajin Ogbomoso ciki da waje

Ya ce a duk wata shari’a da kotu ta ga ya dace don tabbatar da tsaro ko kuma kare bayanan wanda ta shafa ko shaida, za a iya gudanar da ita a duk inda babban alkali ya ayyana tare da kotun da’ar ma’aikata a matsayin wurin gudanar da shari’ar na wani lokaci.

Boko Haram: Mun damke masu daukar nauyin ta'addanci, lamarin zai firgita jama'a, Fadar shugaban kasa

Gwamnatin tarayya ta ce jami'an tsaro sun damke wasu 'yan Najeriya dake daukar nauyin ta'addancin Boko Haram.

Babban mai baiwa shugaban kasa shawara a harkar yada labarai, Garba Shehu, ya sanar da hakan a ranar Talata, 30 ga watan Maris yayin da ya bayyana a shirin siyasarmu a yau na gidan talabijin na Channels.

Legit.ng ta tattaro cewa, Shehu yace jama'a za su matukar girgiza idan suka ji bayanin binciken da ake kan makuden kudin da ake turawa kungiyar.

Ya ce wadanda aka kama sun hada da 'yan canji dake zama a kasashen ketare. Shehu yace:

Kara karanta wannan

Kotu ta sa ranar da za a saurari shari’ar damka Abba Kyari ga hukumomin kasar Amurka

"Yan canji ne ke turawa 'yan ta'adda kudi. Mun riga mun yi aiki da UAE. Mun damke 'yan Najeriya dake turawa 'yan ta'addan Boko Haram kudi kuma lamarin yana faruwa har a cikin gida. Kuma ina sanar daku cewa idan mun gama bincike, sakamakon zai gigita 'yan Najeriya."

'Yan Ta'adda Suna Can Sun Kai Hari A Wani Gari A Jihar Neja, Suna Cin Karensu Babu Babbaka

A wani labarin, 'yan fashin daji suna can sun kai farmaki a garin Daza da ke karamar hukumar Munya a Jihar Niger.

Shaidu, wanda suka tabbatarwa Daily Trust da harin sun ce mutane da dama sun tsere daga gidajensu.

Daily Trust ta tattaro cewa yan bindigan sun kutsa garin ne misalin karfe 5 na yamma kuma suka sace mutane masu yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel