An Bai Wa Hamata Iska Tsakanin Jami’an DSS da Na NSCDC Kan Dalili 1 Tak, Da Dama Sun Samu Raunuka

An Bai Wa Hamata Iska Tsakanin Jami’an DSS da Na NSCDC Kan Dalili 1 Tak, Da Dama Sun Samu Raunuka

  • An bai wa hamata iska tsakanin jami’an DSS da hukumar NSCDC a jihar Edo yayin da DSS su ka kai jami’insu asibiti
  • Lamarin ya faru ne a yau Litinin 4 ga watan Disamba a cikin asibitin kwararru da ke birnin Benin City a jihar
  • Hargitsin ya jawo raunata mutane da dama ciki har da jami’ar hukumar NSCDC da kuma sauran masu gadin asibitin

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo – An samu hargitsi tsakanin jami’an hukumar DSS da kuma jami’an hukumar NSCDC a jihar Edo.

Lamarin ya faru ne a yau Litinin 4 ga watan Disamba a cikin asibitin kwararru da ke birnin Benin City a jihar, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ana jimamin kashe bayin Allah a wurin Maulidi, wani abu ya fashe a jihar APC

An samu hargitsi tsakanin jami'an DSS da na NSCDC
Mutum 2 sun jikkata bayan an kai ruwa rana tsakanin jami'an DSS da na NSCDC. Hoto: DSS/@official_NSCDC.
Asali: UGC

Mene dalilin fadan DSS da NSCDC?

Hargitsin ya fara ne yayin da jami’an DSS su ka kawo dan uwansu zuwa asibitin bayan ya fadi yayin wani taro wanda ma’akatan asibitin ba su musu tarba mai kyau ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Nation ta tattaro cewa an samu daidaito bayan shiga lamarin da shugaban masu tsaron gidan gwamnati ya yi da kuma hukumar ‘yan sanda.

Yayin hargitsin, mutane da dama sun samu raunuka ciki har da masu gadin asibitin yayin da wata jami’ar hukumar NSCDC ita ma ta samu raunuka.

Wani daga cikin jami’an DSS ya bayyana yadda abin ya faru inda ya ce ba su samu tarba mai kyau a asibitin ba inda su ke bukatar kulawar gaggawa.

Wane martani asibitin ta yi?

Ya ce:

“Mu na cikin wani taro ne yayin da daya daga cikinmu ya fadi, mun dauko shi cikin gaggawa zuwa wannan asibitin amma ba su karbe mu da kyau ba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun saki bam sun kashe mutane a wajen Maulidin Annabi SAW a Kaduna

“Mutanen mu ne su ka dauko shi daga cikin mota madadin su ya kamata su yi inda su ka ce ba za su dauko shi ba sai dai mu dauko shi.”

Daraktan asibitin, Dakta David Odiko ya ce jami’an DSS sun ki amincewa sun kawo shi matacce amma likita ya kula da shi har ya fada musu cewa ya mutu.

Dan takarar gwamna ya sha kunya a Edo

A wani labarin, dan takarar gwamnan PDP, Asue Ighodalo ya sha kunya bayan ya gagara magana da yaren da ya ke ikirarin ya fito.

Asue ana sa ran shi ne zai kasance dan takarar gwamnan da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ke muradi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel