Matashi Ya Yi Ajalin Makwabcinsa Saboda Wata 'Yar Hatsaniya Kan Abinci, Mahaifiyarsa Ta Goyi Baya

Matashi Ya Yi Ajalin Makwabcinsa Saboda Wata 'Yar Hatsaniya Kan Abinci, Mahaifiyarsa Ta Goyi Baya

  • Wani matashi ya shiga hannun 'yan sanda bayan zargin hallaka makwabcinsa kan wata hatsaniya saboda abinci
  • Matashin wanda ake zargi mai suna John Edosa ya yi ajalin makwabcin nasa ne mai suna Promise a yankin 'East Circular Road' da ke jihar Edo
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Chidi Nwabuzor ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a birnin Benin City da ke jihar

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Rundunar 'yan sanda a jihar Edo ta cafke wani matashi kan zargin kisan makusancinsa kan abinci.

Wanda ake zargin mai suna Johnson Edosa dan shekaru 21 ya hallaka makusancinsa, Promise mai shekaru 23 saboda hayaniya kan abinci.

Kara karanta wannan

Sojoji sun saki bam sun kashe mutane a wajen Maulidin Annabi SAW a Kaduna

Matashi ya hallaka makwabcinsa kan hayaniya ta abinci a Edo
'Yan sanda sun cafke matashin da zargin kisan makwabcinsa. Hoto: @PoliceNG.
Asali: Twitter

Mene ake zargin matashin da aikatawa?

Daily Trust ta tattaro cewa mutanen biyu na zaune na a yankin 'East Circular Road' inda su ka samu sabani kan abinci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani Edosa ya lallaba da dare tare da yin ajalin Promise da cewa ba shi da cikakken hankali.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Chidi Nwabuzor ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce abin takaici ne.

Chidi ya ce sun samu rahoton faruwar lamarin a ofishinsu da ke St. Saviour kan rikicin tsakanin Edosa da kuma Promise.

Ya ce:

"Wanda ake zargin da marigayin su na zaune ne a gida daya inda Edosa ya yi amfani da wuka ya yanka wuyansa ya na bacci.
"Bayan kisan nashi, mahaifiyar Edosa ta hada baki da shi inda su ka binne mamacin a cikin gidan."

Kara karanta wannan

Dirama yayin da dan takarar gwamnan PDP ya gagara magana da yarensu, ya nemo mai fassara

Wane martani 'yan sanda su ka yi?

Chidi ya sha alwashin hukunta wadanda ake zargin dai-dai gwargwadon abin da su ka aikata wanda ya sabawa kundin tsarin mulki.

Har ila yau, a jihar Edo wani mai dako ya hallaka matashi kan kudin haraji a karamar hukumar Oredor.

Daga bisani wanda ake zargin ya hallaka kanshi a ranar Juma'a 1 ga watan Disamba.

Matashi ya hallaka Kawunsa kan zargin maita

A wani labarin, wani matashi ya hallaka kawunsa har lahira a jihar Adamawa kan zargin maita.

Matashin mai suna John Clackson ya yi ajalin kawun nasa ne mai suna Mohammed Clackson a karamar hukumar Guyuk.

Asali: Legit.ng

Online view pixel