Yan Najeriya Sun Yi Martani Yayin da Yar Sanda Ta Koma Sanya Wa Matar Gwamna Dan Kunne
- Ƴan Najeriya sun mayar da martani daban-daban game da bidiyon da ke nuna wata ƴar sanda ta taimaka wa Titilayo Adeleke, uwargidan gwamnan Osun, wajen sanya ƴan kunnenta
- Bidiyon ya haifar da tattaunawa kan yadda wasu jami'an gwamnati musamman ƴan sanda ba sa nuna ƙwarewa a wajen aikinsu
- Yayin da wasu ke jayayya cewa ya kamata jami'ai su mayar da hankali kan ayyukansu kawai, wasu kuma sun kare matakin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Osun, Osogbo - Wata ƴar sanda mace da ke taimakawa uwargidan gwamnan jihar Osun, Titilayo Adeleke, ta sanya ƴan kunnenta, ta jawo muhawara a yanar gizo.
Bidiyon da aka yaɗa ya janyo cece-kuce kan ayyukan da jami'an tsaron Najeriya suke yi a bainar jama'a.
Bidiyon da wata mai amfani da sunan @MsNemah a X ta sanya, ya sa mutane da yawa suna mamakin yadda Najeriya ta kasance mai tallata bauta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu mutane ƴan kaɗan sun kare matakin, yayin da wasu suka dage cewa ma'aikatan gwamnati kamata ya yi su nuna kwarewa sosai tare da mayar da hankali kan ayyukansu maimakon yin ayyukan da ba na su ba.
Wane irin martani ƴan Najeriya suka yi?
Ƴan Najeriya kamar yadda suka saba sun bayyana ra'ayoyinsu daban-daban kan lamarin. Ga kaɗan daga ciki a nan ƙasa:
@ SimonOthuks ya rubuta:
"Babu wata matsala da wannan joor! Shin za ta ce a'a ne idan uwargidan gwamnan ta roƙe ta ta taimaka? Idan ta ƙi yi nan ma wata matsala ce."
@seunosewa ya rubuta:
"Ƴar sandan ta yi baƙin ciki sosai."
@SIR_CLEMENTIO ya rubuta:
"Za su iya zama ƙawaye."
@Pentastic33 ya rubuta
"Ban yi mamaki ba. Yawancinmu muna tallata ɗabi'ar ubangida/bawa a yawancin ayyukanmu a wannan ƙasa. Ayyukan kamfanoni, wuraren ilimi, hukumomin tsaro, da dai sauransu."
@rotilaw ya rubuta:
"Shi ya sa ba a maganar sake fasalin ƴan sanda."
@OAKay_1 ya rubuta:
"Tunanin samun ƴan kuɗaɗe da tsammanin wani abu da ba dole ba shine dalilin da ya sa jami'an ƴan sanda ke ɗaukar jakunkuna, yin aikace-aikace ga manyan mutanen da suke tare da su."
"Ƙwarewa za ta sanya ka yi asarar ƴan kuɗaɗe, amma za a girmama ka don tsayawa kan ayyukan da aka ba ka na asali. Ka yi tunanin samun horo da ƙare wa a matsayin ɗan aiken gida."
Ɗan Najeriya Ya Jawo Cece-Kuce
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani ɗan Najeriya ya jawo cece-kuce bayan ya kwashi tsabar kuɗaɗe masu yawa domin yin ajiya a banki.
Hoton mutumin wanda ba a bayyana ko wanene ba ya bayyana yayin da ya dauko tulin kuɗaɗe $500,000, da suka yi daidai da Naira miliyan 220 zuwa banki domin ya ajiye.
Asali: Legit.ng