Bidiyon Wani Matashin Yaro Da Yar Yarinya a Otel Ya Haddasa Cece-Kuce

Bidiyon Wani Matashin Yaro Da Yar Yarinya a Otel Ya Haddasa Cece-Kuce

  • Jama'a sun yi cece-kuce bayan bayyanar bidiyon wani matashi dan Najeriya da wata yar yarinya suna shiga wani otal
  • Sai kace ma'aurata, yaron ya rataya hannunsa a wuyan yarinyar sannan suka shige dakin otal din bayan sun tattauna da mai tarbar baki
  • Mutane da dama sun nuna bacin ransu a kan bidiyon sannan suka caccaki masu kula da otal din da suka bar irin wannan abu yana faruwa, wasu kuma sun yi ba a da abun

Wani bidiyon matashi dan Najeriya yana shiga otal da yar karamar budurwa ya haddasa cece-kuce a tsakanin masu amfani da soshiyal midiya.

Wani mai amfani da TikTok, wanda ya wallafa bidiyon, ya nemi Allah ya kare kananan yara masu tasowa, cewa Allah ne kadai zai iya cetonmu.

Matashi ya dauki karamar yarinya zuwa dakin otal
Bidiyon Wani Matashin Yaro Da Yar Yarinya a Otel Ya Haddasa Cece-Kuce Hoto: @trenches_empires
Asali: TikTok

A bidiyon, an rufe fuskar yarinyar da wani katon hoton babi a kokarin boye fuskarta. Bayan ya yi magana da mai tarbar baki na otal din, sai yaron ya sakala hannunsa a wuyan yarinyar yayin da suka shige cikin dakunan.

Kara karanta wannan

Yadda Hoton Rahama Sadau Da Wani Farin Fata Ya Haddasa Cece-Kuce a Soshiyal Midiya

Bidiyon mai tsawon sakan 49 ya fusata mutane da dama inda suka caccaki masu kula da harkokin otal din kan barin kananan yara suna samun masauki a cikinsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wasu sun yi kira ga amfani da lambar NIN wajen ba baki masauki a otal domin tabbatar da ko sun balaga.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan bidiyon kananan yara da suka je otal

Omo Ope ya ce:

"Me yasa aka rufe fuskarta, a bari mutane su ga fuskarta kafin abubuwa su kara muni, saboda irin wadannan yaran ne ake saurin amfani da su, jansu ake yi kamar rakumi da akala."

Eat Exercise & Sleep lifestyle ta yi martani:

"Shiyasa katin shaidar dan kasa ke da amfani a nan don tabbatar da shekarunta."

ASAP RUCKY ya ce:

"Amma wannan bai kamata ba karon farko da na kai yar shekara 20 otal lokacin ina da shekaru 25 tsoro na dunga ji balle kuma wannan karamar."

Kara karanta wannan

“Ya Ga Rayuwa”: Matashi Ya Fara Gasar Kuka Na Awa 100, Ya Sha Alwashin Kafa Tarihi a Duniya

-Chiemelam- ta ce:

"Ni da bana gani na kyale, sai na sha shari'a da mai tarbar bakin, gayen sannan iyaye ko masu rikon yarinyar."

Uba ya kama yaronsa da ya ki makaranta a dakin wata tsohuwar kilaki

A wani labarin, wani bidiyo da ya yadu ya nuno wani matashi dan Najeriya mai shekara 20 wanda ya bar makaranta domin tarewa da wata hajiyar birni mai kudi.

A bidiyon, mahaifin yaron ya nuna rashin jin dadinsa game da halin yaron nasa, yana mai cewa ya so dansa ya je makaranta amma maimakon haka, ya zabi bin wacce ta isa ta haife shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel