El-Rufai, Badaru, Wike Da Sauran Mutane 25 Da Tinubu Ya Nada Minista, Majalisa Za Ta Tantance Su; Kai Tsaye

El-Rufai, Badaru, Wike Da Sauran Mutane 25 Da Tinubu Ya Nada Minista, Majalisa Za Ta Tantance Su; Kai Tsaye

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya iso zauren majalisar tarayya kuma an fara zaman majalisa yayin da yan Najeriya ke jiran jerin sunayen ministocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sabuwar doka da aka yi a Najeriya ta ba wa shugaban kasa kwana 60 ya fitar da ministocinsa kuma wannan wa'adin zai cika zuwa karshen wannan makon.

Lokacin da aka karanto sunayen

Sanata Godswill Akpabio ya karanto jerin sunayen da aka aiko masa, yana farawa da Abubakar Momoh da Yusuf Tuggar CON.

Wasikar da Bola Tinubu ya rubuto ba ta kunshi Jihohin da aka zakulo Ministocin ba.

Sunayen Ministoci

Channels TV ta ce an kawo sunayen mutane 28 da ake so a tantance a matsayin ministoci.

Tinubu da aka karanto a Majalisar Dattawa.

 1. Abubakar Momoh
 2. Yusuf Maitama Tukur
 3. Ahmad Dangiwa
 4. Hannatu Musawa
 5. Uche Nnaji
 6. Betta Edu
 7. Dr. Diris Anite Uzoka
 8. David Umahi
 9. Ezenwo Nyesom Wike
 10. Muhammed Badaru Abubakar
 11. Nasir El-Rufa'i
 12. Ekerikpe Ekp[o
 13. Nkiru Onyejiocha
 14. Olubunmi Tunji Ojo
 15. Stella Okotete
 16. Uju Kenedy Ohaneye
 17. Bello Muhammad Goronyo
 18. Dele Alake
 19. Lateef Fagbemi
 20. Mohammad Idris
 21. Olawale Edu
 22. Waheed Adelabu
 23. Emman Suleman Ibrahim
 24. Prof Ali Pate
 25. Prof Joseph Usev
 26. Abubakar Kyari
 27. John Enoh
 28. Sani Abubakar Danladi

An kawo sunayen Ministoci

A halin yanzu, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Hon. Femi Gbajabiamila ya shigo zauren majalisa dauke da jerin.

Tashar talabijin ta rahoto cewa majalisar dattawa ta ba Femi Gbajabiamila damar shigowa domin ta gabatar da sunayen.

Ana sa ran Akpabio zai karanto sunayen ministocin Tinubu

Akpabio ya iso majalisa misalin kargfe 12.10 na rana sannan ya shiga zauren don fara zama na musamman.

Ana sa ran shugaban majalisar zai karanto jerin sunayen ministocin na Shugaba Tinubu a yau, Alhamis, 27 ga watan Yuli, yayin zaman majalisar.

Akwai alamun cewa a halin yanzu an kawo sunayen ministocin majalisar ta tarayya.

Tinubu, wanda ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Najeriya a ranar 29 ga watan Mayun 2023, yana da kwana 60 bisa kundin tsarin kasa ya fitar da ministocinsa.

Online view pixel