Kurkuku 5 masu hadarin gaske a Najeriya

Kurkuku 5 masu hadarin gaske a Najeriya

- Kurkuku, ko gidan maza ko kuma gidan yari kamar yadda wasu ke fada wuri ne da ko makiyin mutum ba zai yi mashi fatan zuwa ba.

- Wuri ne wanda kuma ya tara kusan wane jinsi, yare da kuma kabila. A kurkuku zaka ga manya zaka ga yaro zaka ga talaka kuma zaka iya ganin mai kudi kai har ma yan siyasa da dai sauransu.

Mafiya yawan manyan kasar nan sun taba zama a kurkuku a wani lokaci na rayuwar su -kama daga shugaban kasa mai ci a yanzu Muhammadu Buhari zuwa Obasanjo.

To ga jerin wasu gidajen kurkuku nan guda 5 masu matukar hadari a Najeria.

1. Kirikiri

Kurkuku 5 masu hadarin gaske a Najeriya
Congested prison conditions in Nigeria

Ita dai wannan yana a garin Apapa ne a jihar Legas. Hakika ya shahara sosai musamman ma saboda yanayin cinkoson sa. Yanzu haka dai anyi amannar cewa yana dauke ne da mutanen da sun fi karfin sa.

KU KARANTA: Za'a sake tuhumar Neymar da Barcelona

Wani abun da yasa yayi karin suna shine yadda ba'a mutunta dan adam a cikin sa.

Mai karatu zai iya tuna cewa a ciki ne aka kulle mutane irin su Chief Bode George, Clifford Orji, Al-Mustapha da Major General Shehu Musa Yar’Adua.

2. Kuje

Kurkuku 5 masu hadarin gaske a Najeriya
Nigerian prisons are dens of dehumanization

Shi kuma wannan yana a babban birnin tarayya Abuja ne. Duk da dai bai yi irin sunan da Kirikiri yayi ba ta fannin cinkoso da kuma cin zarafin bil'adama amma shima dai kam ba daga baya ba.

Shi dai wannan prison din yayi kaurin sunane tun daga shekara ta 1990 inda aka fi sanin shi da garkame yan siyasa da kuma masu sukar gwamnati.

Wadanda aka taba tsarewa ko kuma suke a tsare a wannan kurkuku yanzu haka kuma sun hada da Abba Moro, Olisa Metuh da Nnamdi Kanu.

3. Gboko

Kurkuku 5 masu hadarin gaske a Najeriya
Prisons in Nigeria are better avoided

Shima dai wannan a karamar hukumar Gboko yake a jihar Benue dake a yankin arewa ta tsakiya.

Shima dai wannan gidan yarin ba daga baya ba don kam a cunkushe yake.

4. Jimeta

Kurkuku 5 masu hadarin gaske a Najeriya
Prison Breaks are common due to bad conditions

Shikuma wannan a garin Jimeta yake a jihar Yobe. Wannan gidan yarin yana da matukar hadari don kuma mafi yawan mutanen cikin sa yan Boko haram ne. Wannan ne ma yake cike da hadari don kuwa a kullum cikin zullumi ake don kada yan Boko Haram su kawo mashi hari.

A shekara ta 2012 ma dai akai wani harin inda kusan mutane 40 wanda mafiyawan su yan Boko Haram ne suka tsere.

5. Ibara

Shi kuma wannan gidan yarin a jihar Ogun yake. Wani kazamin al'amari dake faruwa a wannan gidan yarin shine yadda cin hanci da rashawa sukayi katutu inda rahotanni ke nuna cewa wai ma'aikatar gidan har ansar kudi sukeyi daga hannun wadan da aka kulle din don gudanar da ayyukan su.

Wani daga cikin yan kurkukun ya taba shaida wa manema labarai cewa a lokuta da dama sai sun ba ma'aikatan kudin mai sannan ne wai zasu kai su kotu don yi shari'a.

https://youtu.be/KhUBU4G1n0U

Asali: Legit.ng

Online view pixel