Jami'an Tsaro Sun Sheke Dan Bindiga da Ceto Mutum 3 da Aka ace
- An rage mugun iri a jihar Bauchi yayin da jami'an ƴan sanda suka yi artabu da wasu gungun ƴan bindiga
- Jami'an ƴan sandan sun samu nasarar sheƙe wani ɗan bindiga har lahira yayin da sauran suka ranta a na kare
- A yayin artabun jami'an ƴan sandan sun kuma samu nasarar ceto wasu mutum uku da aka yi garkuwa da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Jami’an rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi, sun yi nasarar kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne a yayin wata musayar wuta.
Jaridar Tribune ta ce jami'an ƴan sandan sun halaka ɗan bindigan ne lokacin da yake yunƙurin yin garkuwa da mutane a jihar.
Wata sanarwa daga kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Ahmed Wakili, ta tabbatar da kisan ɗan bindigan, cewar rahoton The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda lamarin ya auku
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"A ranar 29 ga watan Nuwamba da misalin ƙarfe 1:00 wani mutum mai suna Sabitu na ƙauyen Kadade cikin ƙaramar hukumar Toro ya bayar da rahoto cewa a ranar da misalin ƙarfe 12:30 cewa ƴan bindiga sun farmaki ƙauyensu inda suka dira a gidan wani Yakubu Ya’u Makeri na ƙauyen Yagi cikin gundumar Rahama."
"Tawagar ƴan sanda da ke hedikwatar ƴan sanda ta Rishi, tare da ƴan sakai sun yi gaggawar zuwa wurin inda suka yi musayar wuta da ƴan bindigan."
"Jami’an ƴan sandan sun samu galaba a kan ƴan bindigan a yayin fafatawar da suka yi, inda suka kashe ɗaya daga cikin ƴan bindigan yayin da sauran suka tsere."
"Sai dai, a yayin fafatawar, jami’an tsaro sun yi nasarar kuɓutar da mutum uku da aka yi garkuwa da su, waɗanda suka haɗa da: Sunday Ayuba, mai shekara 40, Fasto Bala mai shekaru 50 da Keziya Ayuba mai shekaru 50 waɗanda suka fito daga ƙauyen Raddi na ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Plateau."
Mutanen da aka ceto an yi garkuwa ne da su daga ƙauyukansu da ke jihar Plateau.
Ƴan Bindiga Sun Halaka Mutum Bakwai
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai mummunan farmaki a wasu ƙauyuka biyu na jihar Plateau.
Ƴan bindigan a yayin farmakin da suka kai, sun halaka mutum bakwai tare da yin awon gaba da dabbobi masu yawa.
Asali: Legit.ng