Yan Bindiga Sama da 300 Sun Kewaye Babban Birnin Jihar Arewa, Sun Kashe Jami'an Tsaro Akalla 20

Yan Bindiga Sama da 300 Sun Kewaye Babban Birnin Jihar Arewa, Sun Kashe Jami'an Tsaro Akalla 20

  • Ƙungiyar mafarauta ta koka kan yadda 'yan bindiga sama da 300 suka kewaye Jalingo, babban birnin jihar Taraba
  • Shugaban mafarauta na jihar, Adamu Ɗantala, ya ce kawo yanzu sun kashe jami'an tsaro mafarauta sama da 20
  • Ya yi kira ga gwamnati ta samar musu da makamai da tallafin kuɗi domin tunkarar yan bindiga a lungu da saƙo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Taraba - Shugaban ƙungiyar mafarauta ta jihar Taraba, Adamu Dantala, ya ce wasu yan bindiga sama da 300 sun zagaye Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Mafaraunta sun ce yan bindiga sun kewaye Jalingo.
"Yan Bindiga Sun Kewaye Babban Birnin Jihar Taraba" Mafarauta Sun Koka Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Ya bayyana cewa ƴan bindigan sun gudo ne daga jihohin Zamfara, Bauchi da wasu jihohin kuma sun fara kai hare-haren kauyuka da kwaryar birnin Jalingo.

Kara karanta wannan

Wasu hadimai sun yi jabun sa hannun gwamnan APC don sace kuɗi? Gaskiya ta bayyana

Dantala ya kuma ankarar da cewa waɗannan yan bindiga suke da hannu a yawan garkuwa da mutane a yankunan jihar da kuma wasu sassan babban birnin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindiga sun kashe mafarauta

Kamar yadda Daily Trust ta tattaro, shugaban ƙungiyar mafarautan ya ce kawo yanzu yan bindigan sun halaka mafarauta 22 tare da jikkata wasu yayin da suka yi fito da fito.

A cewarsa, ƴan bindigan ɗauke muggan makamai, sun kashe mafarauta 18 a ƙaramar hukumar Bali kaɗai ranar Talata, cewar rahoton shafin Lindaikeji.

Ya ce:

"Mun ga ɗaruruwan 'yan bindiga a kewayen tsaunuka da cikin dazuka, suna da manyan makamai kuma ga dukkan alamu sun zo ne domin kaddamar da hare-hare kan jama'a."

Abinda ya sa suka fi ƙarfin mu - Dantala

Ya bayyana cewa duk da mafarautan suna da jajircewa da ƙarfin zuciya, amma ba su da manyan makaman da za su tari yan bindigan.

Kara karanta wannan

Luguden wuta: An kashe yan bindiga sama da 50 yayin da suka kai hari a jihar arewa

"Bisa dole mambobinmu suka janye yayin wani artabu da suka yi da 'yan bindiga kwana biyu da suka wuce saboda ba makaman mu ba irin na su bane," in ji shi.

A cewarsa, duk da yakin da suke yi da ‘yan bindiga, ba sa samun tallafin kudi domin baiwa iyalan wadanda aka kashe ko kuma jinyar wadanda suka jikkata.

Shugaban ya yi kira ga gwamnatin jihar Taraba da ta baiwa mafarautan makamai tare da ba su tallafin kudi domin su tunkari ‘yan bindiga a ko ina a faɗin jihar.

Ɗanmodi ya koka kan tabarbarewar tsaro a Jigawa

A wani rahoton na daban Gwamna Namadi na jihar Jigawa ya nuna damuwa kan yadda lamarin garkuwa da mutane ke karuwa duk mako a jihar.

Yayin da ya karɓi bakuncin sabon kwamishinan ƴan sandan Jigawa, Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba zata lamurci lalacewar tsaron a'umma ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel