Hotunan wasu jarirai 2 da aka jefar, ɗaya cikin kwali, ɗaya cikin baƙar Leda a Kebbi
Wasu mutane marasa imani na cigaba da mummunan halin nan na jefar da jarirai, wadanda basu ji ba, kuma basu gani ba, musamman wadanda ake samun su ba ta hanyar halastaccen aure ba.
A nan ma an samu wasu jarirai guda biyu wadanda aka jefar da su a wasu unguwannin daban daban dake garin Birnin Kebbi, na jihar Kebbi, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.
KU KARANTA: Da ɗumi ɗumi: Yan bindiga sun yi garkuwa da fitaccen jarumin Kannywood
Rundunar Hisba ta jihar ne ta sanar da haka, inda ta ce an kawo mata rahoton tsintar jariran ne a ranar Talata 5 ga watan Disamba, inda aka samu daya da ransa, yayin da guda kuma ya rasu.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito an tsinci gawar mataccen ne a unguwar Gesse, daidai bayan ofishin JNI, sa’annan aka tsinci dayan a kan hanyar Bawada, unguwar Gulumbe, duk a cikin garin Birnin Kebbi, kamar yadda shugaban Hisbah, Ibrahim Ahmed ya bayyana.
Wani limamin babban Masallacin Juma’a dake Birnin Kebbi, Sheikh Muhammad Nayilwa ya ja hankalin mutane, tare da gargadin kan cewa kowa zai bayanin abinda ya aikata a ranar Kiyama.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng