Cibiya Ta Wanke Agile Daga Zargin Sheikh Bn Uthman Na Lalata Tarbiyyar Matan Arewa

Cibiya Ta Wanke Agile Daga Zargin Sheikh Bn Uthman Na Lalata Tarbiyyar Matan Arewa

  • Shugabar cibiyar CGE ta yi warware rudanin da aka shiga a game da ainihin ayyukan shirin Agile a Najeriya
  • Habibah Mohammed ta yi jawabi a wajen taron manema labarai da Agile-Katsina ta kira domin a warware rudani
  • Cibiyar CGE ta dauki shekara da shekaru ta na taimakawa wajen bunkasa ilmin mata a jihohin Arewacin kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kaduna - Habibah Mohammed ita ce shugabar cibiyar CGE da ke taimakawa ilmin mata a Arewacin Najeriya, ta yi karin haske game da aikin Agile.

Bayanin ya zama dole ne a sakamakon hudubar da Sheikh Mohammed bn Othman ya yi kwanaki, inda ya ce an fito da tsarin ne domin bata tarbiyya.

Babban malamin ya ce manufar shirin na Agile da aka kawo a jihohin Arewacin Najeriya shi ne bude idanun mata, a raba su da addini da al’adarsa.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya bankaɗo matsala kan yan ta'adda, ya buƙaci a tura ƙarin sojoji zuwa jihohi 6 a arewa

Shugabar CGE
Shugabar CGE. Habibah Mohammed Hoto: Legit
Asali: Original

Tsarin Agile domin 'Yan mata a Najeriya

Cibiyar CGE ta nuna babu abin da ya hada wannan aiki da ke karkashin bankin Duniya da jawo ‘yan mata su raina iyayensu kamar yadda ake tuhuma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hajiya Habibah Mohammed ta ce tun shekarar 2007 CGE ta ke taimakawa ‘yan mata a jihohin Arewacin Najeriya wajen inganta ilmi da zamantakewa.

Cibiyar ta shaidawa Legit da sauran 'yan jarida a wajen taron da Agile-Katsina ta kira a Zariya cewa ana aiki da shugabannin al’umma da malaman addini.

CGE ta na daukar malamai mata domin koyawa ‘yan mata karatun zamani a garuruwan da ta ke aiki a lokacin dalibai ke fuskantar matsaloli.

Me ake koyawa a karkashin Agile?

A cewar Habibah Mohammed, abubuwan da ake koyawa ‘yan matan da ke tasowa sun hada da harkar ilmi, sadarwa, abinci da kuma cin zarafin jinsi.

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa Sun Hadu, An Huro Wuta a Janye Takunkumi, a Maidawa Nijar Kasar Wuta

Makasudin koyar da ilmi shi ne horas da ‘yan mata da nuna masu sanin muhimmancin karatu da hana yara barin makarantun zamani.

Sanin ilmin sana’a, kasuwanci da dogara da kai ya na cikin tsare-tsaren shirin Agile. Sannan akwai batun nau’in abincin da ya dace da ‘yan mata.

Legit ta samu labari a karkashin shirin ne ake koya ilmin lafiyar mata domin wayar da kan su kan cututtukan zamani kamar kanjamu da sauransu.

Mata da-dama sun koyi tsabta da abubuwan da su ka shafi hadarin lalata da maza da daukar juna biyu kafin a je gidan aure wanda ya sabawa addini.

A bangaren yaki da cin zarafin jinsi, shirin Agile ya na koyawa ‘yan mata gujewa mazan banza da burmawa duk wuraren da za su iya shiga hadari.

Kasafin kudin 2024 a Najeriya

Ana da labari Gwamnatin Bola Tinubu ta na hangen Naira Tiriliyan 18 a matsayin abin da zai shigo asusun tarayya cikin kundin kasafin kudin badi.

Ministan kasafin kudi, Atiku Bagudu ya ce an yi karin Naira tiriliyan 1.5 a kasafin shekara mai zuwa daga Naira tiriliyan 26.2 da aka yi lissafi da farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel