Gwamna Zulum Ya Bankaɗo Matsala Kan Yan Ta'adda, Ya Buƙaci a tura ƙarin sojoji zuwa jihohi 6 a arewa

Gwamna Zulum Ya Bankaɗo Matsala Kan Yan Ta'adda, Ya Buƙaci a tura ƙarin sojoji zuwa jihohi 6 a arewa

  • Farfesa Babagana Umar Zulum ya ƙara yin kira ga hukumomin soji su kara turo jami'an soji zuwa jihohin shiyyar Arewa maso Gabas
  • Gwamnan ya bayyana cewa ya kamata sojoji su shiga lungu da saƙo inda yan ta'adda ke fakewa su kakkabe su
  • Zulum ya yi wannan kira ne yayin da ya karbi bakuncin ministan tsaro, Abubakar Badaru da hafsoshin tsaro a Maiduguri

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya yi kira da a tura karin sojoji domin kakkaɓe ‘yan Boko Haram daga matsugunan su a Borno da sauran jihohin Arewa maso Gabas.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umaru Zulum.
Boko Haram: Gwamna Zulum Ya Bukaci a Kara Tura Sojoji Jihohin Arewa Maso Gabas Hoto: Borno APC New Media
Asali: Facebook

Zulum ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin ministan tsaro, Mohammad Badaru Abubakar, da hafsoshin tsaro a Maiduguri ranar Talata.

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa Sun Hadu, An Huro Wuta a Janye Takunkumi, a Maidawa Nijar Kasar Wuta

Ya ce akwai bukatar a samar da tsaro a kan iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, Chadi da Kamaru da ke Arewa maso Gabas, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar gwamnan kare iyakokin zai taimaka wajen hana kwararar mayaƙan ISWAP da kuma shigo da makamai zuwa cikin ƙasar nan.

A rahoton Channels tv, Zulum ya ce:

“Jihar Borno tana da iyaka da Jamhuriyar Kamaru, Chadi da Nijar, don haka ya zama dole mu tabbatar da cewa muna da kwanciyar hankali a jihar."
"Idan ba haka ba, yaduwar kananan makamai da alburusai za su karu kuma mayakan ISWAP zasu yaɗu sakamakon matsalar da ake samu a yankin Sahel. Yankin Sahel shine babbar matsalarmu."
"Saboda haka, muna son ku ƙara ninka ayyukanku da nufin tsaftace gabar tafkin Chadi, dajin Sambisa da tsaunin Mandara."

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan APC zai rubuta takardar murabus daga muƙaminsa, sahihan bayanai sun fito

Zulum ya baiwa hukumomin soji shawara

Gwamnan ya kuma yi kira ga hukumomin sojin kasar da su tura dakaru zuwa lungu da sako na ‘yan ta’addan, wadanda ba su da niyyar miƙa wuya da aje makamai.

"Hakan yana da matukar muhimmanci domin hanya daya tilo da za mu iya kawo karshen ‘yan ta’adda ita ce ta ci gaba da kai samamen soji,” inji shi.

Sabuwar zanga-zanga ta ɓarke a Kano

A wani rahoton kuma Zanga-zanga ta kuma ballewa a jihar Kano ranar Laraba kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Masu zanga-zangar sun fantsama kan tituna suna rera wakokin tir da hukuncin tsige Abba, a cewarsa Kano ta Abba ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel