Ma'adanai Sun Jawo Sabani Tsakanin Dangote da Gwamnati Har An ‘Rugurguza’ Makaranta

Ma'adanai Sun Jawo Sabani Tsakanin Dangote da Gwamnati Har An ‘Rugurguza’ Makaranta

  • Ana zargin kamfanin simintin Dangote da rusa makarantar firamare a karamar hukumar Ewekoro da ke jihar Ogun
  • Zargin da ake yi wa kamfanin shi ne an ruguza wurin karatun saboda an gano akwai albarkatu malale a cikin kasa
  • Gwamnatin Dapo Abiodun ta ce ta hana a taba makarantar kauyen, amma da alama kamfanin bai saurari hukum ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Ogun - Gwamnatin jihar Ogun ta fito ta bayyana cewa ta hana kamfanin simintin Dangote ruguza wata makarantar firamare a garin Elefon.

A ranar Laraba Punch ta kawo labari cewa gwamnatin Ogun ta taka burki da aka nemi ruza makarantar da ke karamar hukumar Ewekoro.

Dangote
Motocin kamfanin simintin Dangote Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

'Dan majalisa ya koka da aikin Dangote

Kara karanta wannan

Yanzu: Kotun daukaka kara ta tsige mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar PDP a arewa

‘Dan majalisa mai wakiltar mazabar Ewekoro, Honarabul Yusuf Amosun, ya fara kokawa kamfanin simintin ya rusa masu makarantar firamare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yusuf Amosun ya zargi kamfanin da rusa wurin karatun saboda zargin sun gano ma’danai da ake amfani da su wajen hada siminti a kamfanin.

‘Dan majalisar ya shaidawa abokan aikinsa cewa ba ayi wa makarantar wani bayani ba, sai kurum kamfanin na Aliko Dangote ya shiga rushe-rushe.

Hon. Amosun ya ce kamfanin bai sanar da ko da hukumomin gwamnati kafin rusa makarantar ba, zargin da ba jaridar Legit ba ta tabbatar da shi ba.

An jawo Majalisa ta soki kamfanin Dangote

Shugaban majalisar dokokin Ogun, Rt. Hon. Olakunle Oluomo ya yi Allah wadai da aikin kamfanin da ke karkashin kulawar Halima Dangote.

Idan dai zargin da ake yi na rusa wuraren karatu saboda hako albarkatun kasa ta tabbata, an rahoto Oluomo ya na cewa sam ba a kyauta ba.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi adalci, ta yanke hukunci kan mutumin da ya daɓawa maƙocinsa wuka har lahira

Gwamnati ta takawa kamfanin Dangote burki?

Kwamishinan ilmi, kimiyya da fasaha na jihar Ogun, Abayomi Arigbabu ya tabbatar da lamarin da jaridar ta zanta da shi a yammacin Talata.

Da aka zanta da Kwamishinan ta salula, ya ce kamfanin ya tare harabar makarantar kwanakin baya, amma gwamnatin Ogun ta tsoma baki.

Arigbabu yake cewa tun makonnin baya Mai girma gwamna Dapo Abiodun ya bada umarni cewa kamfanin simintin ya guji taba makarantar.

Rashin jituwar Dangote da BUA

Kwanakin baya mu ka kawo labari cewa manyan Arewa za su yi sulhu tsakanin Alhaji Aliko Dangote da Alhaji Abdussamad Isiyaku Rabiu.

Bayan rigimar 'yan kasuwan, Shugaban kungiyar NEF, Farfesa Ango Abdullahi ya tsoma bakin rikicin siyasar da ake bugawa a jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng