Kotu Ta Yi Adalci, Ta Yanke Hukunci Kan Mutumin da Ya Daɓawa Maƙocinsa Wuka Har Lahira

Kotu Ta Yi Adalci, Ta Yanke Hukunci Kan Mutumin da Ya Daɓawa Maƙocinsa Wuka Har Lahira

  • Babbar kotun jiha ta ba da umarnin a rataye matashin da ya kashe maƙocinsa har lahira a jihar Ondo
  • Yan sanda sun kama Joseph Abayomi, bisa zargin soka wa makoshinsa dan shekara 63 adda a Akure, babban birnin jihar
  • Bayan doguwar muhawara a tsakanin ɓangarorin biyu, alkali ya ce kotu ta gamsu da hujjojin masu ƙara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - An yanke wa wani mai matsakaicin shekaru, Joseph Abayomi, hukuncin kisa bisa kama shi da laifin halaka maƙocinsa, Thomas Oluwole, a jihar Ondo.

Kotu ta umarci a rataye wanda ya kashe makocinsa har lahira.
Kotun Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Mutumin da Ya Caka Wa Makocinsa Wuka Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, babbar kotun jihar Ondo mai zama a Akure ce ta yankewa wanda ake tuhuma hukuncin kisan ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun rutsa manoma a gonakinsu, sun yi ajalin mutum biyu har lahira a jihar Taraba

Kotun ta ba da umarnin a kashe wanda ake tuhuma bisa kama shi da laifin aikata kisan kai kan maƙocinsa a shekarar 2021 a unguwar Ijoka da ke cikin Akure, babban birnin Ondo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai sun nuna cewa gardama ce ta haɗa makotan biyu kan sanya guba a ruwa, garin haka ne Abayomi ya soka wa mamacin adda a wuya da wasu sassan jikinsa.

Daga baya dakarun ƴan sanda suka damƙe shi bayan samun rahoton abinda ya auku kuma suka gurfanar da shi a gaban ƙuliya kan tuhumar kisan kai.

Yadda aka fafata shari'a a gaban kotu

Yayin zaman sauraron ƙarar, wanda ake zargin ya shaida wa kotu cewa yana cikin hankalinsa a lokacin da ya aikata wannan ɗanyen aiki.

Bayan tafka doguwar muhawara tsakanin lauyoyin masu shigar da kara da masu kare wanda ake tuhuma, kotun ta samu Abayomi da laifin aikata laifin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wa dakarun 'yan sanda wuta, sun halaka rayuka da yawa a jihar APC

A cikin hukuncin da ya yanke, alkalin kotun, Mai shari’a O.S Kuteyi, ya ce ba za a iya wanke Abayomi daga mutuwar Oluwole ba sakamakon abin da ya aikata.

Kuteyi, wanda ya saurari lauyan da ke kare wanda ake tuhuma, ya ce da gangan wanda ake tuhumar ya farmaki mamacin ya sare shi da adda, Punch ta rahoto.

Ya kuma gamsu cewa masu shigar da ƙara sun tabbatar da zargin kisan da ake wa Abayomi, bisa haka alkalin ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An ciro gawar shugaban fulanin da ya ɓara daga cikin rijiya

A wani rahoton kuma An gano gawar shugaban Fulani, Umar Ibrahim, wanda ya ɓata tun ranar Laraba da ta gabata a jihar Filato.

Mai magana da yawun rundunar sojin Operation Save Haven mai aikin wanzar da zaman lafiya a jihar, Kaftin Oya James, shi ne ya tabbatar da ci gaban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel