Halima Dangote da manyan daraktoci 5 sun ajiye aiki daga kamfanin Dangote

Halima Dangote da manyan daraktoci 5 sun ajiye aiki daga kamfanin Dangote

Manyan daraktocin kamfanin Dangote Flour Mills mallakin fitaccen attajiri, Aliko Dangote sun yi murabus daga mukamansu tare da ajiye ayyukansu, domin baiwa yan baya daman shigowa a dama dasu.

Rahoton jaridar Daily Nigerian ta ruwaito shugaban kwamitin gudanarwar kamfanin, Asu Ighodalo tare da wasu manyan daraktocin kamfanin guda 5 ne suka yi murabus, wanda hakan zai bada daman nada wasu sabbin daraktoci guda 4.

KU KARANTA: Kyawun alkawari cikawa: Gbajabiamila ya dauki nauyin jaririya mara lafiya, ya saya mata gida a Katsina

Ita sakatariyar kamfanin, Aisha Isa ta tabbatar da lamarin, inda ta bayyana sunayen sauran daraktocin da suka yi murabus kamar haka; Olakunle Alake, Arnold Ekpe, Yabawa Lawan Wabi, Thabo Mabe, da kuma Halima Dangote.

Ajiye aikin na wadannan daraktoci keda wuya, sai kamfanin ta maye gurabensu da sabbin mutane da zasu cigaba da tafiyar da kwamitin gudanarwar kamfanin da suka hada da Venkataramani Srivathsan, Chandrasekaran Balaji, Mukul Mathur da Anurag Shukla.

A wani labarin kuma, Kaakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya dauki nauyin kulawa da wata jaririya mai suna Halima Abubakar da aka haifa da wata matsalar rashin lafiya a jahar Katsina, inda ya biya mata kudin asibiti a babban birnin tarayya Abuja.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito a kwanakin baya ne Gbajabiamila ya hadu da wannan jaririya a sansanin yan gudun hijira yayin wata ziyara daya kai jahar Katsina, inda ya yi alkawarin daukan nauyin jaririyar, tare da bata kulawar daya kamata.

Mashawarcin Gbajabiamila a kan harkar yan gudun hijira, Hamza Baba, ya bayyana cewa iyayen jaririyar, Abubakar da Nafisa sun fito ne daga kauyen Wagini dake cikin karamar hukumar Batsari a dalilin ayyukan yan bindiga da suka addabi yankin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng