Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama, Ta Yanke Hukunci Kan Zaɓen Gwamnan Jihar Sakkwato

Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama, Ta Yanke Hukunci Kan Zaɓen Gwamnan Jihar Sakkwato

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato a zaben watan Maris, 2023
  • Kwamitin alƙalan kotun ya ce hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zabe ta yanke na korar karar PDP da ɗan takararta ya yi daidai
  • A cewar kotun, masu shigar da ƙara sun gaza gabatar da ƙwararan hujjojin da zasu gamsar kan ikirarin da suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a birnin tarayya Abuja ta tabbatar da nasarar Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato a zaben 2023.

Kwamitin alkalai uku na kotun ne suka yanke wannan hukunci da murya ɗaya ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamba, 2023, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada babban mukami a gwamnatinsa, an bayyana sunansa

Gwamnan jihar Sakkwato, Aliyu Ahmed.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Ahmad Aliyu na Sakkwato Hoto: Ahmed Aliyu
Asali: Facebook

Alkalan karƙashin jagorancin mai shari'a Ita Mbaba, sun bayyana cewa masu shigar da ƙara sun gaza gamsar da kotu da kwararan hujjoji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bisa haka kotun ta kori ƙarar mai lamba CA/S/EP/GOV/SK/30/2023, wadda jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ɗan takararta, Saidu Umar, suka ɗaukaka.

Hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke

Kotun ɗaukaka ƙaran ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe, wadda ta kori ƙarar a ranar 30 ga watan Satumba, 2023.

Mai shari’a Mbaba, a hukuncin da ya yanke, ya ce kotun ta yi daidai da cewa Aliyu da mataimakinsa Idris Gobir sun cancanci tsayawa takara a zaben.

Haka nan kuma alkalin ya bayyana cewa ikirarin masu ƙara cewa gwamna da mataimakinsa sun gabatar da takardun bogi ba gaskiya bane, rahoton Leadership.

Jam’iyyar PDP da Umar, a cikin karar da suka shigar, sun kalubalanci nasarar Aliyu kan cewa gwamna da mataimakinsa ba su cancanci tsayawa takara ba.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun fatattaki yan bindiga a jihar Arewa, sun ceto mutanen da suka sace

Masu shigar da ƙarar sun yi zargin cewa Gwamna Aliyu da mataimakinsa haɗa da ƙarya a takardunsu, kuma an tafka kura-kurai a zaben da ya gabata.

Shugaba Tinubu Ya Sake Nada Mele Kyari a Matsayin Shugaban NNPCL

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya amince da sake naɗa Malam Mele Kyari a matsayin shugaban kamfanin man fetur na ƙasa NNPCL.

Shugaban ƙasar ya kuma naɗa majalisar gudanarwan kamfanin wadda ta ƙunshi Pius Akinyelure a matsayin shugaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262