Tsohon Gwamnan Kano, Bello, Ya Bayyana Abu 1 Tak da Ke Sa Shi Farin Ciki a Rayuwarsa

Tsohon Gwamnan Kano, Bello, Ya Bayyana Abu 1 Tak da Ke Sa Shi Farin Ciki a Rayuwarsa

  • Kanal Sani Bello ya bayyana irin farin cikin daya ke samu wurin saka farin ciki a fuskar talakawa marasa karfi
  • Bello wanda tsohon gwamnan jihar Kano ne ya bayyana haka yayin bikin tiyata kyauta ga marasa karfi a jihar Neja
  • Ya ce babban burinsa a kullum shi ne ya ga farin ciki a fuskar marasa lafiya da ba za su iya yi wa kansu magani ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Neja - Tsohon gwamnan Kano a mulkin soja, Kanal Sani Bello mai ritaya ya bayyana irin yadda ya ke jin dadi idan ya taimakawa marasa lafiya.

Kanal Bello wanda shi ne shugaban Gidauniyar Sani Bello ya bayyana haka ne yayin kaddamar da tiyata kyauta ga marasa lafiya a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan PDP ya daga wa mai gidansa yatsa, ya fito takarar gwamna a jihar

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana abin da ke sanya shi farin ciki a rayuwa
Kanal Sani Bello ya yi martani kan abin da ke sa shi farin ciki. Hoto: FRCN.
Asali: Facebook

Mene Sani Bello ke cewa?

Bello ya ce duk lokacin da ya ga marasa lafiya cikin farin ciki bayan an biya musu kudin jinya ya na jin dadi a ransa, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gidauniyar ta gudanar da jinyar ce kyauta da hadin gwiwar Gidauniyar Graceland Health Development a karamar hukumar Kontagora da ke jihar.

Ya roki masu hannu da shuni da su rinka taimakon marasa karfi ba tare da nuna bambanci ba, cewar Voice Newspaper.

Ya kara da cewa ya na jin dadin ganin farin cikinsu musamman daga jihohin Kano da Legas da Katsina da Sokoto da Imo da Akwa Ibom.

Tsohon gwamnan ya ce ya gwammace ya yi amfani da bikin haihuwarsa wurin taimakon talakawa madadin hada babban biki.

Wane martani Gidauniyar Graceland ta yi?

Har ila yau, ya bayyana hada babban biki don gudanar da bikin ranar haihuwa a matsayin bata lokaci.

Kara karanta wannan

Sheikh Bala Lau ya yabawa Uba Sani kan 'inganta walwalar' mazauna Kaduna

Shugaban Gidauniyar Graceland, Dakta Tohot Dogo ya ce a cikin shekaru 10 da su ke hadaka sun yi wa mutane dubu 13 tiyata inda ya ce tiyatar ta shafi ta bangaren ido.

Uba Sani ya yi kyauta ga masu musabaka

A wani labarin, Gwamna Uba Sani ya yi alkawarin babbar kyauta ga wadanda su ka lashe gasar musabaka a jihar.

Ya ce mutum biyu da su ka yi nasara a bangaren mata da maza za su samu shiga cikin jerin malamai ma su fadakarwa a aikin hajji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.