Rashin Fahimtar Turanci Ke Sa Cewa Akwai Kuskure a CTC, Kperogi Ya Zargi Alakai Kan Hukuncin Kano
- Yayin da ake ci gaba da tofa albarkacin baki kan fitar da takardun CTC, Farfesa Farouk Kperogi ya yi martani kan matsalar
- Kperogi ya ce wadanda ba sa fahimtar Turanci ne kawai za su kira hakan da kuskure a ciki daman haka hukuncin ta ke
- Farfesan ya ce ya tabbata alkalan kotun sun yi hukunci ne ba tare da duba hukuncin karamar kotun ba a baya
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Farfesa Farouk Kperogi ya yi martani kan fitar da takardun CTC da kotun daukaka kara ta yi a Kano.
Kperogi ya ce babu wata maganar kuskure a cikin takardun CTC da kotun ta fitar da ya jawo cece-kuce, Legit ta tattaro.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/9b05b9cddd1edae4.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Shari’ar Kano: Gwamna Abba ba zai maida takardun hukuncin kotu ba Inji Lauyan NNPP
![Kperogi ya yi martani kan kuskuren takardun CTC a jihar Kano Kperogi ya yi martani kan kuskuren takardun CTC a jihar Kano](https://cdn.legit.ng/images/1120/1bed101a5e57f3c5.jpeg?v=1)
Asali: Facebook
Mene Kperogi ke cewa kan hukuncin Kano?
Farfesan ya ce ya tabbata alkalan kotun sun yi hukunci ne ba tare da duba hukuncin karamar kotun ba a baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce daga bisani an samu wasu abubuwa da su ka sha bam-ban da hukuncin wanda hakan ya tilasta su sake rubuta hukuncin nasu.
Ya ce:
“A yayin sake rubuta hukuncin nasu, sun yi fatali da hukuncin karamar kotun a baya wanda hakan ya jawo cece-kuce."
Kperogi ya bayyana ma'anar kuskure
Ya kara da cewa:
“Wannan kuskure da su ke magana ba komai ba ne illa burbudin kura-kurai a baya, wadanda ba sa fahimtar Turanci ne za su kira hakan kuskure.”
Kperogi ya ce ta yaya za a ce wai takardun CTC an yi kuskure a ciki, ba zai yiwu ace dukkan abin da aka rubuta kuskure ba ne.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/940013e45c6d7207.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Kano: Alkalai 'yan Adam ne ba ma'asumai ba, APC ta fadi yadda za a gyara bayan fitar CTC
Ya ce abin da ake kira da kuskure shi ne rubuta wani abu ko harafi wanda hakan ba zai sauya komai a shari’ar ba.
‘Yan sanda sun gargadi APC, NNPP kan zanga-zanga
A wani labarin, rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta gargadi magoyan bayan jam’iyyun APC, NNPP kan gudanar da zanga-zanga a jihar.
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin yin zanga-zanga bayan fitar da takardun CTC da su ka jawo cece-kuce.
Asali: Legit.ng